Atiku Ya Fada Mana Ayyuka 8 Da Ya Yiwa Arewa Lokacin Yana Mulki: Kashim Shettima
- Kashim Shettima ya kalubalanci dan takarar shugaban kasan jam'iyyar PDP ya fito fili ya amsa wasu tambayoyi
- Shettima ya ce yan Arewa su daina cewa zasu zabi Alhaji Atiku Abubakar saboda dan Arewa ne
- A cewar tsohon gwamnan na Borno, babu abinda Atiku ya tsinanawa Arewa lokacin da yake mulki
Sokoto - Dan takaran kujerar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress APC, Kashim Shettima, ya caccaki dan takarar shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar.
Shettima ya ce masu cewa zasu zabi Atiku kawai don dan Arewa ne basu san wanene dan takaran PDPn ba.
Ya kalubalanci Atiku ya fadawa yan Najeriya ayyukan takwas da ya yiwa Arewa lokacin da ya rike kujerar mataimakin shugaban kasa tsawon shekaru takwas.
Shettima ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa a filin kamfen APC a jihar Sokoto ranar Alhamis.
A cewarsa:
"Atiku ya yi shekara 8 a matsayin mataimakin shugaban kasa, ya kirga ayyuka takwas da ya yiwa Arewa. Ya kirga mutum 8 da ya gina a Arewa."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Naka, naka ne amma ba nakan da ya san aljihunsa kadai ba."
Lokacin sakawa Tinubu Alherin da yayi ya iso
Kashim Shettima ya bayyana cewa idan al'ummar Arewa bata zabi Tinubu ba basu kyauta ba.
Ya ce zai zama butulci saboda Tinubu ya goyi bayan yan Arewacin Najeriya tun zamanin Yar'adua, Nuhu Ribadu, Atiku da kuma Buhari a 2015.
Shettima ya lissafo yadda Tinubu ya sanya al'ummar yankin kudu ta yamma suka ka'dawa Buhari kuri'a a zaben 2015.
A cewarsa:
"A 2015, Kasar Yarabawa da Edo da Tinubu ke jagoranta suka bamu kuri'u miliyan 2 da muka kayar da Jonathan da su.
"Lokacin sakamako ya yi, mu hada karfi da akrfe, mu cire kanmu daga kunya, a sanmu da kunya da dattaku."
"Jama'a a takaice, Allah ya ce a Suratul-Rahman: Sakamakon Alheri, Alheri ne."
"Mu nuna cewa yan Arewa masu amana ne, Tinubu ya yi mana hallaci."
Abinda zamu yiwa yan Najeriya
Shettima ya ce idan suka smau nasara a zaben 2023, zasu inganta rayuwan mutanen Najeriya.
"Idan Allah ya bamu mulki, zamu rike amana, zamu kula da al'umma."
"Zamu samawa dubban matasa abun yi, za'a tallafawa yan kasuwa, zamu share hawayen malaman boko da islamiyya."
..Yace.
Asali: Legit.ng