Ku Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Kudadenku, Zamu Bi Umurnin Kotun Koli: Gwamnatin Tarayya
- Gamayyar jam'iyyun siyasa a Najeriya ta ce jam'iyyar APC na kokarin amfani da kotu wajen cimma manufafofinta
- Jam'iyyar PDP, LP da NNPP sun ce basu amince a dage wa'adina daina amfani da Naira ba duk da wahalar da yan Najeriya ke ciki
- Ana cigaba da samun mabanbantan ra'ayi game da hukuncin kotun koli da ta yanke a cigaba da amfani da tsaffin Naira
Gwamnatin tarayya ta saduda game da wa'adin daina amfani da tsaffin takardun Naira da ya kamata ya zama yau Juma'a, 10 ga watan Febrairu, 2023.
Gwamnatin ta bayyana cewa babu komai za ta bi umurnin kotun kolin Najeriya da ta dakatad da shirin hana mutane amfani da tsaffin kudadensu fari daga ranar 10 ga Febrairu.
Zaku tuna cewa kotun koli a ranar Laraba ta dakatad da shirin haramtawa mutane amfani da tsaffin kudinsu yau Juma'a, 10 ga Febriaru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Antoni janar kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, ya bayyana cewa babu komai zamu bi umurnin.
A hirar da yayia tashar Arise TV, ya ce suna kyautata zaton cewa kotun za tayi watsi da karar ranar Laraba, 15 ga wata.
Ya ce dalili kuwa shine bankin CBN bai cikin wadanda aka shigar a karan, saboda haka kotun koli ba tada hurumin sauraron karar.
Ya ce za su bi umurnin kotun ne kawai saboda gwamnatin Buhari na ganin girma da mutuncin doka.
Ku cigaba da amfani da kudinku, idan Tinubu ya hau zai soke dokar Buhari kan Tsaffin Naira: El-Rufa'i
A wani labarin kuwa, Gwamna Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna ya baiwa gamayyar yan kasuwar jiharsa cewa su kwantar da hankulansu, kuma su ajiye tsaffin kudinsa kada su kai banki.
Malam El-Rufa'i ya bayyana hakan ne yayin zama da yan kasuwa tare da dan takarar gwamnan jihar na APC, Uba Sani.
A cewarsa, duk me tsaffin kudi ya kawo masa zai saboda Tinubu na hawa mulki zai soke dokar da Buhari yayi.
Antoni janar ya yi kira ga kotun kolin tayi soke hukuncin da tayi na baiwa yan Najeriya dama cigaba da amfani da tsaffin kudi.
Asali: Legit.ng