Har Dajin Sambisa Za'a Gudanar Da Aikin Kidaya a 2023 - Hukumar Kidaya Ta Kasa

Har Dajin Sambisa Za'a Gudanar Da Aikin Kidaya a 2023 - Hukumar Kidaya Ta Kasa

  • Gwamnatin tarayya ta jaddada shirinta na gudanar da kidayar yan kasa bayan kammala zaben 2023
  • Rabon da a gudanar da kidaya a Najeriya tun shekarar 2006 lokacin mulkin Olusegun Obasanjo
  • Hukumar ta bayyana cewa ta shiga lunguna da sakon kasar nan kuma kowa za'a kirga

Abuja - Hukumar kidaya ta kasa ta bakin shugabanta, Nasiru Isa Kwarra, ya bayyana cewa hukumar zata gudanar da aikin kidaya har cikin dajin na Sambisa dake Arewa maso gabas.

Ya kara da cewa duk da yake akwai kalubale na tsaro, hukumar tasu zata tabbatar da cewa an kidaya mutanen da suke zaune a wannan dajin.

Ya bayyana hakan ne a bikin rantsuwar kama aiki na kwamatin yada labarai na aikin kidaya na kasa a Abuja, rahoton Punch.

Census
Har Dajin Sambisa Za'a Gudanar Da Aikin Kidaya a 2023 - Hukumar Kidaya Ta Kasa
Asali: Getty Images

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da tankar ta fadi ta fashe, hukumar ta bayyana halin da ake ciki

"Zan tabbatar da cewa an kidaya yankin. Babu wani lungu da bamu ziyarta ba. Ma'aikatan mu sun shiga kauyuka da suke fama da matsalar tsaro fiye da dajin Sambisa, saboda haka, ina mai tabbatar muku da cewa babu wani wanda za'a bari a cikin shirin kidayar."
"Kuma duk wani muhimmin waje an tabbatar da daukar bayanan sa tare da sanya masa alama a taswirance. Wannan kudiri shine ya bada damar samun nagartattun tsare tsare da tabbatar da ingantattun shirye shirye a kidayar da ta gabata a shekarun baya.
"Duk da wannan, muhimmancin tabbatar da bin tsarika, yada labarai akan wannan shiri tare da wayar da kan jama'a bazai misaltu ba." .

Ya kara da cewa hukumar duba da cewa ayyukan dake a gabanta za ta ilimantar da yan Najeriya muhimman bangarori da aikin kidayar ya kunsa kamar kidaya duk wani mutum dake zaune a Najeriya a lokacin da ake gabatar da aikin kidayar kamar dai yadda za'a kidaya kowanne gida da magidanta a fadin kasa.

Kara karanta wannan

Canjin Kudi: Makiya Dimokradiyya Ne Ke Son Kawo Rudani A Najeriya, In Ji Tinubu

Ko Sambisa kaje za ka ga sabbin kudi, Emefiele ya bayyana dalilin rashindage wa'adin tsaffin Naira

Godwin Emefiele, na babban bankin Najeriya CBN, ya bayyana cewa ko dajin Sambisa aka shiga yanzu za'a tarar da sabbin takardun Naira.

Emefiele ya ce bankin ya tura mutane 30,000 da zasu taimakawa mutane wajen canza tsaffin kudadensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida