Jami'an Tsaro Sun Damke Sanatan Da Ake Nema Ruwa a Jallo, An Jefashi Kurkuku a Legas
- Bayan wata da watanni ana wasar buya tsakaninsa da jami'an EFCC, an damke Sanata Nwaboshi
- Nwabosho Sanata ne mai wakiltar mazabar Delta ta Arewa ma majalisar dattawan Najeriya
- Sanata Peter dan jam'iyya mai gwamnati ne watau jam'iyyar All Progressives Congress APC
Jami'an hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta damke danata Peter Nwaboshi bayan watanni ana nemansa ruwa a jallo.
Nwabosho ya yi layar zana bayan kotun daukaka kara dake jihar Legas ta yanke masa hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari bisa almundahanar kudi.
An jefa shi gidan yari a Legas, rahoton Leadership.
Mai magana da yawun hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce sun damke Nwaboshi ne a wani asibiti ranar Litinin, 6 ga Febriaru, 2023.
Yace a ranar Laraba, 8 ga Febrairu suka jefashi gidan yarin don ya fara zamansa da aka yanke masa.
Uwujaren ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar yau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukuncin kotu kan Nwaboshi
Kotun daukaka kara a hukuncin da ta yanke ranar 1 ga Yuli, 2022 ta yankewa Nwaoboshi hukuncin daurin gidan yari kan tuhumar almundahanr kudi.
Hakazalika kotun ta yi umurnin rufe kamfanoninsa biyu, Golden Touch Construction Project Ltd da Suiming Electrical Ltd, kuma ya sadaukar da dukiyarsa ga gwamnatin tarayya.
Maimakon zuwa kotu ranar, Nwaoboshi yayi layar zana kuma ya shigar da kara kotun koli inda ya bukaci ayi watsi da karar kuma a bashi beli.
Amma a ranar 27 ga Junairu, 2023, kotun koli ta yi watsi da bukatarsa. Alkalin kotun, Emmanuel Agim, yace ta wani dalili zai ki bin umurnin kotun daukaka kara.
Alkali Tijjani Abubakar, a gudunmuwarsa ya ce Sanatan ya rainawa kotun wayau ta hanyar neman beli daga wajenta yayinda ya ke wasan buya da hukuma.
Matsaloli Sun Dabaibaye Kasa: Shugaba Buhari Zai Jagoranci Zaman Majalisar Magabatan Najeriya Yau Juma'a
Ana neman matar gwamna: Kotu ta tura jinin gwamna Yahaya Bello gidan yari kan zargin badakalar N3bn
A wani labarin kuwa, hukumar EFCC ta gurfanar da dan'uwa gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello gaban kotu bisa almundahana da babakere.
An gurfanar da Ali Bello ne kare da Abba Adauda, Yakubu Siyaka Adabenege, Iyada Sadat da Rashida Bello da ake nema bisa zargin aikata laifuka 18 na sama da fadin N3,081,804,654.00.
Asali: Legit.ng