Shugaba Buhari Ya Kori Shugaban Hukumar NSITF Daga Aiki Kan Abu 1
- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sauke shugaban asusun Inshora na Najeriya (NSITF), Michael Akabogu
- Wani ma'aikaci a NSITF ya tabbatar da an sauke shugaban domin ci gaba da bincike kan zargin da ake masa na bogin shaidar NYSC
- Rundunar 'yan sanda na bincike kan takardar da yake amfani da ita ta gama bautar ƙasa kuma NYSC ta ce Satifiket din ba nata bane
Abuja - Bayanai sun nuna cewa an sallami babban Daraktan Asusun Inshora na ƙasa (NSITF), Mista Michael Akabogu, daga aikinsa.
Har yanzu babu cikakken bayani kan dalilin da ya sa aka kori dataktan NSITF daga aiki amma wasu bayanai da aka tattara sun nuna cewa matakin ba zai rasa alaƙa da zargin bogin takardar shaidar bautar ƙasa (NYSC) da ake masa ba.
Wata majiya mai karfi a NSITF, wacce ta tabbatar da lamarin ga jaridar Daily Trust, ta ce an umarci ya sauka daga kujerarsa ne kafin gama bincike da 'yan sanda suke a kansa.
"Eh, an umarci ya sauka daga mukaminsa," inji wani ma'aikaci a hukumar wanda ya nemi a ɓoye bayanansa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin da aka nemi jami'ar hulɗa da jama'a ta NSITF, Misis Ijeoma Oji-Okoronkwo, ba'a same ta ba har zuwa yanzun da muke haɗa wannan rahoton, wayarta a kashe.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa hukumar 'yan sanda ta gayyaci shugaban NSITF, mai mallakin takardar shaidar gama aikin bautar ƙasa A030544 bayan shigar da ƙorafi a kansa.
Hukumar NYSC ta kasa, a wata wasika da ta aike wa rundunar 'yan sanda mai lamba NYSC/CCD/VER/10/S.1/VOL/07, ta nesanta kanta da Satifiket ɗin wanda Akabogu ke ikirarin na shi ne.
IMF Ya Shawarci Buhari da CBN su kara wa'adin amfani da tsaffin Naira
A wani labarin kuma Asusun ba da lamuni na duniya ya tsoma baki kan wa'adin daina amfani da tsoffin takardun naira da CBN ya sauya
IMF ya bukaci CBN ya ɗaga wa'adin daga 10 ga watan Fabrairu, saboda ganin yadda kasuwanci da hada-hadar kuɗin hannu suka rushe sakamakon sabon tsarin.
Wannan na zuwa ne awanni bayan Kotun koli ta dakatar da CBN daga haramta takardun tsohon kuɗin nan da kwana 2.
Asali: Legit.ng