Bankuna Na Samun N30m A Kullum?: Jami'in CBN Ya Bayyana Adadin Sabbin Naira Da Bankuna Ke Samu A Kullum

Bankuna Na Samun N30m A Kullum?: Jami'in CBN Ya Bayyana Adadin Sabbin Naira Da Bankuna Ke Samu A Kullum

  • Sababbin rahotanni sun bayyana yadda babban bankin kasa ke raba miliyan 1 kullum ga reshen bankuna a Lagos
  • Rahoton ya kuma bayyana cewa kudin baya isar bankuna da suke da miliyoyin abokan hulda da kuna daruruwan rassa a jihar
  • Wani jami'in CBN ya bayyana cewa suna bada miliyan 30 ga kowanne banki a Najeriya

Babban bankin kasa, CBN ya bayyana cewa yana baiwa kowanne reshen banki naira miliyan 1 na sababbin kudi.

Rahotanni sun bayyana cewa, adadin bazai ishi masu hulda da bankuna a jihar da ke da miliyoyin masu ajiya da ke bin dogayen layukan ATM suna jiran sabon kudi.

New Notes
Bankuna Na Samun N30m A Kullum? Jami'in CBN Ya Bayyana Adadin Sabbin Naira Da Bankuna Ke Samu A Kullum. Hoto: National Archive
Asali: Getty Images

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babban bankin yayi shiru kan takamaiman adadin da suke baiwa bankuna

Kara karanta wannan

CBN: Mun Gano Wani Banki Sun Boye Miliyoyin Kudi na Makonni, Ana Karancin Naira

Wani mai fashin baki ya bayyana cewa ko dai CBN basu da wadatattun kudi ko kuma suna hana kudin da gangan ga bankuna ba tare da wani dalili ba.

Koma menene, yanayin ya janyo tsananin wahala ga yan Najeriya da ke tururuwa a ATM.

Sannan, suma bankunan sun ki bayyana adadin da babban bankin ya ke ba su a sati.

Wani ma'aikacin Sterling Bank, wanda ba a bayyana sunan shi ba, ya ce miliyan 1 ake bawa kowanne reshen banki a Lagos.

''Wannan dalilin ne ya sa mu ke bada sabon kudi a kullum.

Reshen bankunan mu basu kai na sauran bankuna yawa ba, amma muna saka kudin a ATM kuma muna biya akan kanta,'' kamar yadda majiyar ta shaida wa Legit.ng

Bankuna suna tsoron bayyana abin da suke karba daga CBN a sati saboda tsoron kada a hukunta su

Haka, suma CBN ta ki bayyana adadin da ta ke baiwa bankuna a duk sati.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda ICPC Ta Farmaki Banki, Ta Bankado Sabbin Naira Boye a Durowa

Abdulkadir Jubrin, wani jami'in CBN a Jihar Bauchi ya ce bankuna suna karbar naira miliyan 30 kullum kowanne reshe, kamar yadda Punch ta ruwaito.

CBN bata karyata ko tabbatar da ikirarin Jubrin din ba.

Masu hada-hadar POS a Jigawa Sun Mika Godiya Ga Babban Bankin Najeriya

A wani rahoton kun ji cewa mutane masu sana'ar POS sun mika godiya ga babban bankin Najeriya, CBN, saboda tsari da ya fito da shi na ba su sabbin kudi N500,000 a duk rana domin su cigaba da sana'arsu.

Hakan na zuwa ne bayan CBN din ya saka dokar kayyade cire N20,000 daga bankuna a kowanne rana.

Adadin kudin da ake cirewa kowanne rana baya ya isar mutane da dama yin hada-hadar da suka saba hakan ya janyo dogon layi a wuraren POS da bankuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164