Karancin Naira: Gwamnan Jihar Oyo Ya Dakatad da Kamfensa Bayan Zanga-Zangar da Ta Barke a Jihar

Karancin Naira: Gwamnan Jihar Oyo Ya Dakatad da Kamfensa Bayan Zanga-Zangar da Ta Barke a Jihar

  • Ba tare da bata lokaci, gwamna ya dakatad da yakin neman zabensa biyo bayan kai hari ofishinsa, rahoton TVC.
  • Matasa, direbobin motocin haya, da mata sun bazu a titunan Ibadan, birnin jihar don zanga-zanga
  • Sun koka kan wahalar rayuwar da suka shiga sakamakon karancin Naira da tsadar man fetur

Ibadan - Gwamnan jihar Oyo, Oluseyi Makinde, ta sanar da dakatad da harkokin kamfen neman tazarcensa sakamakon zanga-zangar da ta barke a fadin jihar.

A ranar Juma'a, fusatattun matasa sun barke da zanga-zanga a garin Ibadan bisa wahalar rayuwar da karancin Naira ya haddasa tare da tsadar mai.

Makinde ya ce dakatad da kamfen ya zama wajibi ne saboda soyayyar da yake wa al'ummarsa bisa tsanani da wahalar da gwamnatin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta jeda jama'ar ciki, rahoton Guardian.

Kara karanta wannan

Ba gama da tuna abin da ya faru a Katsina da Kano ba, Buhari ya kai ziyara wata jihar Arewa

MAkinde
Karancin Naira: Gwamnan Jihar Oyo Ya Dakatad da Kamfensa Bayan Zanga-Zangar da Ta Barke a Jihar
Asali: Twitter

Kwamishanan labaran jihar, Dr. Wasiu Olatubosun, ya ce gwamnan da kansa ya sanar da dakatad da komai da komai yayinda yake garin Ido don kamfe, riwayar Leadership.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dr. Wasiu Olatubosun ya ce:

"A matsayin girmamawa jama'ar jihar Oyo, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bada umurnin dakatad da dukkan harkokin yakin neman zaben jam'iyyar a fadin jihar har zuwa ila maa shaa'a LLahu."

Fusatattun matasa sun kai hari ofishin gwamna yayin zanga-zanga

Mumunar zanga-zanga ta barke a Ibadan, babbar birnin jihar Oyo sakamakon halin kunci, tsadar kaya, da kuma rashin takardun Nairan siya a Najeriya.

Hotuna da bidiyoyi sun nuna yadda fusatattun matasa sun tare hanyoyi suna kone-konen tayoyi.

TheNation ta ruwaito cewa matasan sun kai hari ofishin gwamnan jihar, Seyi Makinde.

Har direbobin motocin haya ba'a bari a baya ba wajen zanga-zangar.

Kara karanta wannan

Ku Cigaba da Bin Layi Ba Zamu Kara Wa'adin Naira Ba Bayan Ranar 10 ga Febrairu, Gwamnan CBN

Kalli hotuna da bidiyoyin:

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida