Karancin Naira: Irin barnar da fusatattun matasa suka yi Banki a Ibadan

Karancin Naira: Irin barnar da fusatattun matasa suka yi Banki a Ibadan

  • Da alamun zanga-zangar da ya ta barke a garin Ibadan yau Juma'a ta fara daukan sabon salo
  • Bidiyo ya nuna yadda wasu fusatattun matasa suka fara kai hare-hare bankuna fushin rashin samun kudi
  • Gwamnatin tarayya ta tilastawa mutane kai kudadensu banki amma yanzu sun gaza cirowa

Da alamun abubuwa na neman tabarbarewa inda fusatattun matasa suka fara bayyana fushinsu kan karancin takardun kudin Nairan da jefa rayukan mutane da kasuwancinsu cikin wani hali.

Bidiyo ya nuna matasa sun fara kai hari bankin Wema dake garin Ibadan sakamakon rashin samun iya cire kudinsu.

Da farko matasan sun fara zanga-zangan ne a cikin birnin Ibadan inda suka tare hanyoyi sun kona tayoyi.

Daga bisani suka garzaya gidan gwamnatin jihar kuma suka nufi fasawa ofishin gwamnan jihar.

Bidiyo ya nuna yadda matasa suka fasa na'urar ATM guda don neman kudi.

Kara karanta wannan

Hukumar yan sanda ta yi magana game da mutumin da ya mutu a layi ciki banki

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wema Bank
Karancin Naira: Fusatattun Matasa Sun Kai Mumunan Hari Banki a Garin Ibadan
Asali: Twitter

Wani ma'abobin Tuwita mai suna Oyindamola ya daura bidiyon yadda matasa ke jifan wani banki a garin Ibadan.

A cewarsa:

"Wannan shine bankin Wema dake Ibadan kuma fusatattun matasa na kan kai hari yanzu saboda sun gaza samun kudadensu daga bankin... da alamun gwamnati na farin cikin wahalar da mutane"

Diraktar sadarwa na kungiyar yan wasan Nollywood a Najeriya, Kate Henshaw ta daura bidiyon barnar da akayi a shafinta na Tuwita.

Ta bayyana cewa:

"Kun ga irin abinda ke faruwa idan aka kai mutane bango."

Karancin Naira: Fusatattun Matasa Yan Zanga-Zanga Sun Kai Hari Ofishin Gwamna

Mumunar zanga-zanga ta barke a Ibadan, babbar birnin jihar Oyo sakamakon halin kunci, tsadar kaya, da kuma rashin takardun Nairan siya a Najeriya.

Hotuna da bidiyoyi sun nuna yadda fusatattun matasa sun tare hanyoyi suna kone-konen tayoyi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Budewa Dan Takaran Gwamnan Jihar Ebonyi Wuta, An Kashe Direbansa

TheNation ta ruwaito cewa matasan sun kai hari ofishin gwamnan jihar, Seyi Makinde.

Har direbobin motocin haya ba'a bari a baya ba wajen zanga-zangar.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida