Buhari ya Bukaci 'Yan Najeriya Su Bashi Kwanaki 7 Don Shawo kan Matsalar Sabbin Kudi

Buhari ya Bukaci 'Yan Najeriya Su Bashi Kwanaki 7 Don Shawo kan Matsalar Sabbin Kudi

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya roki 'yan Najeriya da su bashi kwanaki bakwai domin yanke hukunci kan karancin sabbin kudin da ake fama da shi
  • Ya sanar da hakan ne yayin ganawa da Gwamnonin APC a fadarsa ta Aso Villa a ranar Juma'a, ana tsaka da batun musayar naira
  • Shugaban kasan ya ce zai koma wurin babban bankin Najeriya da kamfanin buga kudi, za su yanke hukunci kafin cikar wa'adin

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci 'yan Najeriya da su bashi kwanaki bakwai kacal domin ya shawo kan matsalolin da suka kawo karancin sabbin takardun kudi.

Gwamnonin APC da Buhari
Buhari ya Bukaci 'Yan Najeriya Su Bashi Kwanaki 7 Don Shawo kan Matsalar Sabbin Kudi. Hoto daga Thecable.ng
Asali: UGC

Shugaban kasan yace ya ga rahotanni da ke nuna karanci da kuma illar da rashin kudin ya janyowa kasuwanci da jama'a talakawa.

Yace ragowar kwanaki bakwai daga cikin goma da aka kara kan wa'adin amfani da sabbin kudin za a yi su ne ana shawo kan matsalolin da suka hana nasarar tabbatar da tsarikan sabbin kudin.

Kara karanta wannan

Kuyi Hakuri Da Wahalar Karancin Naira Kamar Yadda Kuke Hakuri Da Shan Magani Idan Baku Da Lafiya: Ministar Kudi

"Zan koma kan babban bankin Najeriya da kamfanin buga kudi. Za a yanke hukunci a cikin ragowar kwanaki bakwan nan da aka kara."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Shugaban kasan ya tabbatar a ranar Juma'a.

Ya bayyana matsayarsa ne yayin da ya gana da gwamnonin Najeriya da ke karkashin inuwar jam'iyya mai mulki ta APC.

Sannan a wallafar da shugaban kasan yayi a shafinsa na Twitter, yace ya san halin matsain da 'yan Najeriya suka shiga sakamakon musayar takardun kudin.

Matsalar dai rashin tsabar kudi na cigaba da kamari a cikin gari wanda lamarin ke durkusar da san'ao'i masu tarin yawa a Najeriya.

Hakan ya biyo bayan rashin kudin a injinan bayar da kudi na bankuna da kuma rashin bayar da kudin da ma'aikatan bankunan ke yi.

Legit.ng Hausa ta gano yadda farashin kayayyaki a kasuwanni ballantana na kauye suka fadi warwas duk saboda rashin tsabar kudin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC Zasu Shiga Ganawar Sirri Da Buhari Kan Lamarin Naira Da Tsadar Mai

Kamar yadda aka gano, 'yan kasuwan sun karya farashin kayayyakin da kusan kashi hamsin duk don su samu tsabar kudin don biyan wasu bukatu nasu, sai dai ba a samun masu siyan baki daya.

A zantawar Legit.ng Hausa da Malam Habu, wani 'dan kasuwar Hatsi da ke karamar hukumar Dandume ta jihar Katsina, ya sanar da cewa kudin tsaba ya ke nema don bai yadda da batun tiransifa ba, amma kuma babu kudin.

Yace ya shirya zabge farashin kowanne daga cikin hatsin da ya ke da su da suka hada da gero, dawa, masara da wake matukar zai samu kudin rabin buhu saboda yana matukar matse da bukatar kudin.

Gwamnonin APC sun fada ganawar sirri da Buhari

A wani labari na daban, gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki sun shiga ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sun shiga ganawar ne a safiyar Juma'a, 3 ga watan Fabrairu yayin da ake cikin matsin rashin tsabar kudi a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng