Wasu Tsagerun ’Yan Bindiga Sun Sace Kwamishinar Mata Na Cross River

Wasu Tsagerun ’Yan Bindiga Sun Sace Kwamishinar Mata Na Cross River

  • Rahoton da muke samu daga jihar Cross River ya bayyana cewa, an sace wata kwamishina mai ci a jihar
  • Ganau ya bayyana cewa, an sace matar ne da karfi a lokacin da wasu matasa suka farmaki motarta a Calabar
  • Ya zuwa yanzu dai jami’an tsaro sun fara aikin ceto da kamo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki

Calabar, jihar Cross River - ‘Yan bindiga sun sace Gertrude Njar, wata kwamishinar harkokin mata a jihar Cross River da ke Kudancin Najeriya.

An sace Njar ne a ranar Laraba 1 ga watan Fabrairun 2023 a Calabar, babban birnin jihar, The Cable ta ruwaito.

Rahoton kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN) ya naqalto wani ganau da ya bayyana cewa, an tafi kwamishinar ne da karfi lokacin da wasu matasa suka farmake ta a motarta.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Daba Sun Yi Garkuwa da Ɗan Takarar Gwamnan APC a 2023

An sace kwamishinar mata a jihar Cross River
Wasu Tsagerun ’Yan Bindiga Sun Sace Kwamishinar Mata Na Cross River | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

An ce ‘yan bindigan sun tafi da ita ne a motarsu, inda suka bar motarta kuma a wurin da lamarin ya faru a yankin Calabar ta Kudu a jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hukuma ta tabbatar da faruwar lamarin

Kalita Aruku, mai ba gwamna Ben Ayade shawari kan harkokin yada labarai ya tabbatar da faruwar lamarin, rahoton Daily Nigerian.

An ruwaito shi yana cewa:

“Tabbas, majiyoyin tsaro sun sanar da mu cewa an sace kwamishinar harkokin mata.
“Da muke magana, jami’an tsaro sun fara aikin farautar masu garkuwa da mutanen tare da nufin kamo su da ceto wacce aka sace ba tare da wata illa ba.”

Ana yawan samun hare-haren ‘yan bindiga a yankin Kudancin Najeriya, musamman a cikin shekarun nan da suka gabata.

Babu yankin da ya tsira a Najeriya da ba a samun munanan lamuran satar mutane da neman kudin fansa.

Kara karanta wannan

Assha: Dan takarar majalisa a jam'iyyar su Kwankwaso a Arewa ya sace N681m daga asusun banki

'Yan IPOB sun kashe jami'ar 'yan sanda a jihar Imo

A wani labarin, kunji yadda rundunar 'yan sandan jihar Imo ta zargi 'yan ta'addan IPOB da sheke wata jami'arsu da ke aiki a jihar.

An ruwaito cewa, wannan lamari ya faru ne yayin wata musayar wuta da aka yi tsakanin jami'an 'yan sanda da kuma 'yan ta'addan IPOB da ke addamar mutanen jihar Imo.

Rundunar ta sha alwashin kamo masu laifin tare da hukunta su daidai da tanadin dokar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.