Dubun Wata Mata Ta Cika, an Kama Ta Yayin da Take Siyar da Sabbin Naira a Twitter

Dubun Wata Mata Ta Cika, an Kama Ta Yayin da Take Siyar da Sabbin Naira a Twitter

  • Yayin da karancin sabbin kudi ke ci gaba da zama matsala ga ‘yan Najeriya, an samu wasu da ke siyar da sabbin Naira a kasar
  • An kama wata mata da ta yi bajekolin siyar da kudade a kafar Twitter, wanda ya kai ga gano wasu boyayyun batutuwa
  • Hukumomin ICPC, EFCC da babban bankin Najeriya (CBN) na ci gaba da mai da hankali ga tabbatar sabuwar dokar kudi ta Najeriya

Najeriya - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ya kwamushe wata mata mai suna Omoseyin Oluwadarasimi Esther da ke siyar sabbin Naira a kafar Twitter, Leadership ta ruwaito.

Matar mai shafin Twitter da sunan @Simisola ta bude sabuwar harkallar siyar da kudaden ne a shafinta na Twitter kafin ta gamu da bacin rana.

Kakakin hukumar ICPC, Azuka Ogugua ya bayyana cewa, an kama matar ne bayan samun bayanan sirri na yadda take harkallarta, hakan kuma ya kai ga nasarar kwamushe ta.

Kara karanta wannan

Assha: Dan takarar majalisa a jam'iyyar su Kwankwaso a Arewa ya sace N681m daga asusun banki

Yadda aka kama matar da ke siyar da kudi a Twitter
Dubun Wata Mata Ta Cika, an Kama Ta Yayin da Take Siyar da Sabbin Naira a Twitter | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

ICPC ta ce, matar, wacce take kasuwancin man gyaran fata, harkallar man fetur, shirya sufuri zuwa kasashen da dai sauran sana’o’i ta yi amfani da damar karancin sabbin kudi don bude kasuwar siyar da kudi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda matar ke samu kudi take siyarwa jama’a

Kakakin na ICPC ya kuma bayyana cewa, an gano matar na da wasu jami'an banki da ke ba ta sabbin Naira a madadin rabawa mutane.

Hakazalika, bayanai sun nuna wasu bankuna na ba da kudaden ga 'yan kasuwar bayan fage sabanin rabawa mutane a cikin banki, rahoton Aminiya.

A cewar kakakin na ICPC:

“A yanzu haka an tsare Oluwadarasimi a hannun ICPC kuma tana taimakawa hukumar wajen gano tushen wannan mummunan harkalla na Naira da ma karancinsu da kuma matsalar tattalin arziki da hakan ke jawowa.
“Aikin ana yinshi ne tare da hadin gwiwar CBN, ICPC da EFCC don tabbatar da sabon ka’idar kudi da kuma sauya fasalin Naira.”

Kara karanta wannan

Sabon salo: 'Yan jihar Arewa sun koma amfani da kudin wata kasa a madadin Naira

‘Yan Najeriya sun koma amfani da CFA a madadin Naira

A wani labarin kuma, kunji yadda karancin Naira ya kai ga wani sabon salo a Najeriya, ‘yan kasar sun sauya zane wajen neman kudin amfanin yau da kullum.

Wani rahoton da ya fito ya bayyana cewa, wasu mutane a jihar Sokoto sun koma amfani da takardun CFA na jamhuriyar Nijar.

CBN da sauran hukumomin tsaro na ci gaba da sa ido kan masu harkallar sabbin Naira da kuma boye kudaden a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.