Ministan Jonathan Ya Fadawa Kotu Yadda Aka Wawuri Kudin B/Haram Domin Kamfe

Ministan Jonathan Ya Fadawa Kotu Yadda Aka Wawuri Kudin B/Haram Domin Kamfe

  • Musiliu Obanikoro ya bayyana a matsayin shaida a shari’ar Hukumar EFCC da Ayodele Peter Fayose
  • Tsohon Ministan tsaron kasar ya sanar da kotu umarnin da Sambo Dasuki ya ba shi a lokacin yana NSA
  • Sanata Obanikoro ya ce daga asusun kudin da ake yakar Boko Haram, aka fitar da kudin yi wa PDP kamfe

Lagos - Tsohon karamin Ministan tsaron Najeriya, Musiliu Obanikoro ya fadawa kotun tarayya umarnin da Kanal Sambo Dasuki mai ritaya ya ba shi.

Leadership ta rahoto cewa ana shari’a tsakanin hukumar EFCC mai yakar masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa da Mista Ayodele Peter Fayose.

Da aka koma kotun tarayyar mai zama a Legas a makon nan, tsohon Ministan tsaron ya ce Sambo Dasuki ne ya umarce shi ya ba Ayodele Fayose N1.2bn.

Kara karanta wannan

Sabon Tsari: CBN Ya Ƙara Shigo da Abu 2 da Zasu Rage Wa 'Yan Arewa Wahalar Neman Sabbin Kuɗi

A wancan lokaci Fayose yana Gwamna a Ekiti, kuma an cire kudin ne daga wani asusu na musamman da aka ware domin a yaki kungiyar Boko Haram.

EFCC ta kira shaidu a kotu

Sanata Obanikoro ya yi magana a matsayin shaidan da Lauyoyin EFCC suka gabatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana tuhumar tsohon Gwamnan na jihar Ekiti da badakalar N3.2bn, wanda daga ciki N1.2bn sun fito ne daga wani asusun da ke karkashin kulawar NSA.

Jonathan
Sambo Dasuki da Goodluck Jonathan Hoto; Getty Images
Asali: Getty Images

Punch ta ce Fayose da kamfaninsa Spotless Investment Limited su na amsa laifuffuka 11 da suka shafi cin amana, sata, da taba dukiyar al’umma.

Sambo Dasuki ya bar sako?

Da aka gayyace shi domin bada shaida, Obanikoro ya ce a Yunin 2014 ana shirin zaben Gwamnan Ekiti, Fayose ya tuntube shi ko Dasuki ya bar masa sako.

Jim kadan bayan wayar salular sai ga wasika daga ofishin NSA, ana umartar karamin Ministan ya aika wasu kudi daga asusun da yaki da Boko Haram.

Kara karanta wannan

Assha: Dan takarar majalisa a jam'iyyar su Kwankwaso a Arewa ya sace N681m daga asusun banki

Sahara Reporters ta ce kudin sun fito daga akawun din ofishin na mai bada shawara a kan tsaro zuwa wani kamfani mai suna Silver Maclamaran Nigeria Ltd.

Lauyan EFCC, Rotimi Jacobs SAN ya matse bakin ‘dan siyasar har ya shaida cewa N2.2bn aka cire daga asusun NSA, aka warewa PDP a zaben Gwamna a Ekiti.

Harin Shugaban kasa

A wani jawabi da aka fitar a ranar Laraba, kun samu labari cewa Jam’iyyar APC tayi magana kan abin da ya faru da Muhammadu Buhari a garin Kano a makon nan.

Duk da PDP tayi tir da abin da aka yi wa shugaban na Najeriya, amma APC ta ce ‘Yan adawar ne suka kai wa tawagarsa hari, ta kuma bukaci jami’an tsaro su bincika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng