Musanya Sabbin Kudi: CBN Ya Shigo da Bankunan Microfinance da Masu POS a Zamfara
- CBN ya kara bullo da sabbin hanyoyin da mutane zasu samu sabbin takardun naira a jihar Zamfara
- Kwanturolan babban bankin na jihar, Abbas Buhari, ya ce sun shigo da bankunan Microfinance da masu POS cikin tsarin musaya
- A ranar Lahadi da ta gabata ne gwamna CBN ya sanar da kara wa'adin daina amfani da tsoffin kuɗi da kwana 10
Zamfara - Domin bunkasa shirin musaya, babban bankin Najeriya (CBN) yace ya jawo bankunan Microfinance da masu POS cikin tsarin musanya wa mutane kuɗi a yankuna masu haɗari na jihar Zamfara.
Channels tv ta tattaro cewa yankunan da abin ya shafa suna karkashin kananan hukumomin Zurmi, Shinkafi, Birnin Magaji da Maru.
Kwanturolan bankin CBN reshen Zamfara, Abbas Buhari, ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a Gusau, babban birnin jihar ranar Laraba.
Yayin da yake jawabi, Kwanturolan ya jaddada cewa mafi yawan kuɗin da kowane mutum zai iya musanya wa ya ba da tsoffi a ba shi sabbin naira shi ne N10,000.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yace:
"Mu nan a CBN mun riga mun yi tsari domin tabbatar da sabbin takardun naira sun isa wurin mutane a kuyukan Zamfara, musamman wuraren da matsalar tsaro ta yi wa katutu."
"Babban bankin Najeriya ya ɗauki wasu bankunan Microfinance da masu POS a kananan hukumomi uku, Zurmi, Birnin Magaji da Shinkafi, sai kuma garin Ɗansadau a Maru, inda ake ganin matsalar ta fi yawa."
"Naira dubu 10,000 ne mafi yawan kuɗin da mutum ɗaya zai iya musanya wa ya ba da tsoffi a ba shi sabbin takardun naira."
Wannan ci gaban na zuwa ne awanni bayan gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele, ga sanar da ƙara wa'adin musanya kuɗin daga 31 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Fabrairu, 2023.
Punch ta tattaro cewa an ƙara wa'adin ne domin ƙara ba mutane damar samun sabbin kuɗin yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da bin dogon layi da fatan samun kuɗin.
CBN Ya Gano Sabbin Kudi Har Miliyan N4m Makare a Cikin Bankuna a Ogun
A wani labarin kuma CBN Ya Gano Masu Ɓoye Miliyoyin Sabbin Kudi, Ya Fadi Abinda Ya Dace Mutane Su Yi
Wani Babban ma'aikacin CBN ɗin, wanda ƙarara ya nuna fushinsa, ya zargi Bankunan kasuwanci da yi wa kokarin babban banki na samar da isassun kuɗin ga al'umma zagon ƙasa.
Asali: Legit.ng