Yanzu Yanzu: Bankuna Za Su Ci Gaba Da Karbar Tsoffin Kudi Bayan Cikar Wa’adin CBN, Inji Emefiele

Yanzu Yanzu: Bankuna Za Su Ci Gaba Da Karbar Tsoffin Kudi Bayan Cikar Wa’adin CBN, Inji Emefiele

  • A yau Talata, 31 ga watan Janairu ne gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele ya gurfana a gaban majalisar wakilai don yi mata bayani kan manufofin CBN
  • Emefiele ya ce bankuna za su ci gaba da karbar tsoffin takardun kudi ko bayan cikar wa'adin da CBn ya diba na daina amfani da su
  • A ranar 10 ga watan Fabrairu ne wa'adin kwanaki goma da bankin ya kara daina amfani da tsoffin kudi zai cika

Abuja - Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya ce bankuna za su ci gaba da karbar tsoffin kudi bayan cikar wa’adin da aka duba.

Emefiele ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 31 ga watan Janairu lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai, jaridar The Cable ya rahoto.

Kara karanta wannan

Dalibar Jami'ar Abuja Ta Bankawa Dakin Kwanan Dalibai Wuta

Godwin Emefiele
Yanzu Yanzu: Bankuna Za Su Ci Gaba Da Karbar Tsoffin Kudi Bayan Cikar Wa’adin CBN, Inji Emefiele Hoto: @cenbank
Asali: Twitter

CBN za ta karbi tsoffin kudade daga wajen bankuna

Ya ce CBN ma za ta karbi tsoffin kudin daga hannun bankuna bayan cikar wa’adin 10 ga watan Fabrairu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Emefiele ya yi nuni ga dokar CBN wanda ya wajabtawa babban bankin ci gaba da karbar tsoffin kudi har bayan cikar wa’adin da ya diba na daina amfani da su.

A wata sanarwa da majalisar ta yi a shafinta na twitter ta jaddada matsayin gwamnan babban bankin kasar, inda ta nakalto yana fadin cewa:

"Bisa amincewa da shawarar majalisar wakilai da sashi na 20 (3) wanda ya ce ko bayan tsoffin kudin sun rasa martabarsu na halastattun kudi an umurcemu da karbar wadannan kudade. Za mu ci gaba da karbar tsoffin kudade a asusun banki."

Garuruwan karkara na shirin komawa ga cinikayya irin na da

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: Ta rincabe tsakanin Buhari da 'yan majalisa kan sabon wa'adin daina amfani tsohon kudi

A wani labarin kuma, wasu garuruwan karkara sun fara tunanin komawa ga tsarin cinikayya na 'bani gishiri na baka manda' yayin da ake ci gaba da samun karancin sabbin kudi a kasar.

A yanzu dai kasuwanci na fuskantar gagarumin kalubale domin dai jama'a na gudun karbar tsoffij kudi yayin da wa'adin CBN na daina amfani da su ke kara gabatowa.

Mutane da dama sun rufe kasuwancinsu yayin da wasu suka shigar da kudinsu asusun banki wasu kuma sun siya kaya wadanda za su siyar idan kudin ya zaga gari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng