Mambobin ISWAP Sun Rabawa Fasinjoji Tsofaffin Takardun Naira Kan Babban Titin Borno
- Wasu da ake zargin mayakan ta'addanci na ISWAP ne sun raba makuden kudi ga jama'a da ke kan babban hanyar Maiduguri a jihar Borno
- Sun saka kayan sojoji tare da ajiye buhun kudi inda suka dinga raba N100,000 ga kowanne fasinjan motocin da suka tsare tare da cewa su canza zuwa sabbin kudi
- Wata majiya ta sanar da yadda kowa da ke cikin motarsu ya samu N100,000 kuma suka yi musu addu'ar Allah ya saka musu albarka a cikinta
Borno - Wasu da ake zargin mabobin kungiyar ta'addanci ta ISWAP ne sun raba makuden kudade ga jama'a da ke wucewa ta hanyar Tafkin Chadi kafin zuwan ranar da tsofaffin takardun naira za su fara aiki, majiyoyi suka tabbatar.
Daily Trust ta tattaro cewa, lamarin ya faru ne a kauyen Mairari da ke kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Munguno a ranar Asabar a karamar hukumar Guzamala ta jihar Borno.
Wata majiya ta sanar da Daily Trust a Maiduguri cewa, mambobin ISWAP din sun yi shigar sojoji tare da tuka manyan motocin yaki biyu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani mazaunin yankin mai suna Bakura Ibrahim, yace 'yan ta'addan sun tsara kansu a karkashin wata bishiya yayin da wasu suka tsaya gefen titi da tsofaffin takardun kudin.
"Mun bari Munguno wurin karfe 12 na rana. Yayin da mu ke tunkarar Mairari, mun ga babu sojoji a kan hanya, lamarin da yasa muka saka ayar tambaya.
"Sun tsayar da mu inda suka tambaye mu ko Maiduguri za mu je. Daga nan suka fara baiwa kowanne daga cikin N100,000 amma mun kasa yadda. Sun ba duk wanda ya ke cikin motar mu kirar Golf Volkswagen."
- Bakura yace.
Wata majiya ta kara da cewa:
"Kungiyar ta sanar mana cewa, idan kuna tunanin za ku iya zuwa bankunansu kuma ku canza zuwa sabon kudi, ku je yanzu. Allah ya saka muku albarka a ciki."
Ganduje ya ziyarci Buhari, yace Kanawa sun Shirya karbar bakuncinsa
A wani labari na daban, bayan shugaba Buhari ya kara wa'adin daina karbar tsofaffin kudi a Najeriya, Gwamna Ganduje da tawagarsa daga Kano sun ziyarci Shugaba Buhari a garin Daura.
Sun yaba masa ka yadda ya ji koken jama'a tare da share musu kuka ta yadda ya kara wa'adin daina karbar tsofaffin takardun kudin kasar nan.
Asali: Legit.ng