CBN Ya Fara Musanya Wa Mutane Sabon Kudi a Jihar Sakkwato
- Babban banki ya fara musanya wa mutane masu karamin karfi tsaffin kudi da sabbi a jihar Sakkwato
- Kwanturolan CBN reshen jihar, Dahiru Usman, ya shawarci yan Najeriya game da wa'adin kwana 10 da aka ƙara
- A ranar Lahadin nan gwamnan CBN ya sanar da kara wa'adin daina amsar tsohon kuɗi zuwa 10 ga watan Fabrairu
Sokoto - Babban bankin Najeriya (CBN) ya fara shirin musanya wa mutane kuɗi su ba da tsoho a basu sabbbin takardun Naira uku da aka sauya a jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya.
Kwanturolan CBN reshen jihar Sakkwato, Dahiru Usman, ya shawarci mutane da su yi amfani da karin kwana 10 su musanya tsoffin N200, N500 da N1000 da sabbi.
Channels tv ta rahoto cewa Kwanturolan ya baiwa mutanen shawaran ne a yankin Gumbi, ƙaramar hukumar Wamakko, jihar Sakkwato yayin shirin musaya da CBN ya tsiro da shi.
Ya kuma buƙaci ɗaukacin al'umma su taimakawa gwamnatin tarayya ta cimma kudirinta na takaita yawon takardun kuɗi domin amfanar talakawa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mista Usman ya yi bayanin cewa babban Banki ya bullo da shirin musayar ne domin mutanen kauye su samu damar musanya tsaffin kuɗinsu da sabbi cikin sauki.
A cewarsa, mazauna karkara zasu amfana da shirin kasancewar nan ne babu rassan bankunan kasuwanci, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Bugu da ƙari, Kwanturolan CBN a Sakkwato ya bayyana shirin musanyar a matsayin wata dabara ɗaya tilo da zata tabbatar mutanen ƙauye sun samu sabbin takardun kuɗi.
Abinda 'yan Najeriya ke cewa game da sabon shirin
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa babban bankin ya fara wannan shirin a jihohi da dama kuma mutane na samun kuɗin ba tare da shan wahalar zuwa banki ba.
Yayin da wakilinmu ya ziyarci wurin musayar a garin Dabai, ƙaramar hukumar Ɗanja, ya ga yadda mutane suka yi layi suna jiran a masu musaya.
Ɗaya daga cikin mutanen dake jiran layi ya zo Kansu, Muhammad Bello, ya shaidawa wakilin Legit.ng Hausa cewa wannan tsarin abu ne mai kyau ga marasa karfi.
Bello, yace mutane na zuwa da 'ya'yansu sannan su sanya su a layi saboda N10,000 da ake musanya wa sun masu kaɗan.
"Gaskiya wannan tsari ya yi, zai taimakawa talakawa, amma na fahimci mutane ba zasu bari kowa ya samu ba, muna yaba wa CBN," inji shi.
Wakilinmu ya fahimci kudin sun kare bayan mintunan da ba su wuce 60 ba, amma wani magidanci, Babani Sa'adu ya shaida cewa yana zargin 'yan siyasa da hana ruwa gudu.
"Ban samu musayan ko kwandala ba amma ina zargin yan siyasa da hannu a karewar kuɗin, sai da suka fara zuwa sannan aka ce tsabar sabbin kuɗin sun kare, ya kamata su bari mu samu kuɗin nan."
A wani labarin kuma Wasu yan Najeriya sun maida martani bayan CBN ya kara wa'adin kwana 10 kafin rufe amsar tsaffin kuɗi
Wasu mazauna babban birnin tarayya Abuja sun nuna farin ciki da jin dadi bayan kara wa'adin musanya tsohon kuɗi da sabon da aka canja.
Wannan na zuwa ne bayan shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da bukatar CBN na ƙara kwanakin dawo da kudaden.
Asali: Legit.ng