Sabbin Kuɗi: CBN Ya Sha Alwashin Sanya Ido Kan Manyan Dakunan Ajiya Na Bankuna

Sabbin Kuɗi: CBN Ya Sha Alwashin Sanya Ido Kan Manyan Dakunan Ajiya Na Bankuna

  • CBN ya sha alwashin sanya wa manyan ɗakunan bankuna ido domin magance ɓoye sabbin kuɗi
  • Kwanturolan CBN na jihar Ribas, Mista Maxwell Okafor, ya ce Bankuna na zaluntar jama'a wajen sakin sabon kuɗi
  • Yace yan POS ba su samun takardun sabon kudin kuma su ne masu shiga lungu da sako

Rivers - Babban Bankin Najeriya (CBN) yace zai sa ido sosai kan manyan ɗakunan ajiye kuɗi na Bankunan 'yan kasuwa a jihar Ribas da nufin gano bankunan da ke ɓoye sabbin takardun kuɗi.

Jaridar Daily Trust ta rahoto CBN na cewa zai ɗauki wannan matakin ne domin magance ɓoye sabbin kuɗi da ke jefa 'yan Najeriya cikin wahala.

Babban Bankin Najeriya.
Sabbin Kuɗi: CBN Ya Sha Alwashin Sanya Ido Kan Manyan Dakunan Ajiya Na Bankuna Hoto: CBN
Asali: UGC

Kwanturolan CBN reshen Jihar Ribas, Mista Maxwell Okafor, ne ya bayyana haka a Patakwal bayan duba yadda shirin musayar kuɗi ke gudana a Patakwal da Igwurita, ƙaramar hukumar Ikwerre ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Bayan Kara Wa'adi, CBN Ya Sake Fitar da Sanarwa Mai Muhimmanci Ga Yan Najeriya

Mista Okafor yace da yawan mutane musamman masu sana'ar POS suna shan wahala matuƙa kafin su samu sabbin kuɗin kuma hakan ya sa kudin ba su zuwa ƙauyukan da babu Banki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa masu POS suna shan bakar wahala kafin su samu sabbin kuɗin kuma da yawansu sun karaya sun daina zuwa Bankuna domin tsayuwa suke na tsawon awanni.

Meyasa CBN zata sa iso kan Bankuna?

Kwanturolan CBN na Ribas ya ƙara da bayanin cewa idan suna sa ido kan manyan dakunan ajiyan Bankuna zai kawo ƙarshen boye sabbin kudi da sauya masu hanya.

"Yana daukar dogon lokaci kafin mu shiga Banki mu taimaka wa masu POS su samu sabbin kuɗi. Idan har 'yan Najeriya zasu sha fama irin haka a gabanmu ya kuke tunani idan bamu kusa?"
"Ya kamata bankuna su saukaka wa yan Najeriya ta yadda zasu samu sabbin kuɗin cikin sauki musamman masu POS. Masu POS ke kai kuɗi wuraren da babu Banki, ta hannunsu kuɗi ke shiga lungu da saƙo."

Kara karanta wannan

Saura Kwana 2 Wa'adi Ya Cika, CBN Ya Ɓullo da Shirin Yadda 'Yan Arewa Zasu Samu Sabbin Kuɗi Cikin Sauki

"Game da ɓoye sabon kuɗi, zamu kara zage dantse domin tabbatar da kuɗaɗen sun isa hannun mutane. Zamu je har ɗakuna, mu sa ido kan yadda suke rabawa, me gare su da kuma ATM."

- Maxwell Okafor.

Mun karbi tsoffin kudi Tiriliyan N1.9tr, Saura N900bn a hannun Mutane, CBN

A wani labarin kuma Babban Bankin Najeriya ya ce tsarin canja kudi ya haifar da ɗa mia ido, da yawan kudi sun dawo Bankuna

Godwin Emefiele, ya bayyana cewa jumullan tsoffin kuɗi Tiriliyan N1.9trn sun dawo hannun bankuna, abinda ya rage bai wuce N900bn ba a hannun Jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262