Buhari ya Nada Sabon Shugaban Hukumar NYSC Bayan Sauke Fadah da Wata 3
- Shugaba Buhari ya nada Birgediya Janar Dogara Ahmed a matsayin sabon darakta janar na hukumar NYSC
- A hukumance, ranar Litinin 30 ga Janairun 2022 ne Dogara zai karba ragamar hukumar daga hannun Christy Uba
- Tun a watan Nuwamban 2022, Buhari ya fatattaki Birgediya Janar Fadah daga shugabancin hukumar bayan rashin kwazo a shekarar
FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Birgediya Janar Dogara Ahmed matsayin sabon darakta janar na hukumar NYSC.
Dogara a hukumance ranar 30 ga watan Janairun 2023 zai shiga ofis inda zai karba ragama daga Christy Uba, wanda ke jagorantar lamarin hukumar na tsawon watanni uku, jaridar Leadership ta rahoto.
Uba, wacce ita ce babban daraktan hukumar, an nada ta mukaddashi bayan tsige Birgediya Janar Mohammed Fadah Kan Zargin rashin kwazo a 2022.
A ranar 22 ga watan Nuwamban 2022, NYSC ta sanar da karin girma ga daraktan yada labarai da sadarwa, Christy Uba zuwa mukaddashin darakta janar na hukumar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Premium Times ta rahoto cewa, ta kafa tarihin zama mace ta farko da ta samu wannan matsayin tun bayan kafa hukumar a shekaru 50 da ta gabata.
Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na hukumar, Eddy Megwa, yace nadin ya biyo bayan sauke Birgediya Fadah matsayin darakta janar da shugaba Buhari yayi.
Ana baje-kolin sabbin kudi a Zaria, masu siyar da kudi suna shan kasuwa
A wani labari na daban, wasu masu harkar siyar da sabbin kudi suna cin karensu babu babbaka inda suke siyar da sabbin takardun Naira da aka Canza.
An gano cewa, lamarin na faruwa ne a tashar Dadi da ke Sabon Gari ta Zaria a jihar Kaduna.
Kamar yadda aka gano, suna siyar da duk bandir daya na N1000 kan N130,000 ma’ana ana karin N30,000 kan kowanne bandir din N1,000.
A kowanne bandir din N500 ana siyar da shi kan N70,000 wanda ake kara N20,000 matsayin riba.
A yayin da aka zanta da masu wannan sana’ar da ke karantsaye ga dokokin babban bankin Najeriya, sun ki yin magana ko karin bayani.
Wata ‘yar kasuwa ta sanar da cewa, dole ce tasa ta nemi canjin saboda gudun lalacewar kudin baki daya.
Asali: Legit.ng