Saura ranar aiki 1 kacal, CBN Tace Ta Fitar Da Sabbin Kudi N120m Jihar Katsina
- Saura kwanaki biyu kacal wa'adin da gwamnatin tarayya ta sanya kan tsaffin Naira ya kare
- Daga ranar 31 ga watan Junairu, 2023, duk wanda bai sauya kudinsa zuwa sabbi ko a kai banki ba zai yi asara
- Shugaba Muhammadu Buhari ya yiwa yan Najeriya alkawarin cewa zai yi mai yiwuwa don kawo sauki kan lamarin
Katsina - Ofishin babban bankin Najeriya CBN dake jihar Katsina ya fitar da sabbin kudi N120 million ga wakilan bankuna a jihar.
Wannan ya biyo bayan ziyarar shugaba Muhammadu Buhari jihar inda ya kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jihar ta kammala.
Bankin ya ce an yi hakan ne domin saukakewa mutane masu kudi kasa da Naira dubu goma sauya tsaffin kudadensu zuwa sabbi yayin wa'adin ranar 31 ga Junairu, 2023 ya matso, rahoton ChannelsTV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Diraktan harkokin kudi na CBN, Ahmed Bello Umar, wanda ke jihar Katsina domin ganin yadda lamarin ke gudana a ranar Asabar ya ce bankin ya tura jami'ansa bibiyan yadda ake raba kudaden.
Ya yi bayanin cewa aikin wadannan jami'ai ya hada da bibiyan na'urorin ATM don tabbatar da cewa akwai kudade cikin don mutane su cira.
A cewarsa, ATM za ta baiwa mutane damar cire kudi.
Umar ya yi kira ga mutane su shigar da karan duk bankin da yaki budewa ko kuma bai bada sabbin kudi wajen CBN don a hukuntasu.
A cewarsa:
"Mun tattauna da wakilan bankuna a jihar Katsina; muna da wakilan bankuna hudu inda muka bada N120 million don rabawa."
"Ya kamata wakilan su karbi N500,000 a mako domin rabawa garuruwan da babu isassun bankuna. Hakazalika mun kara wani tsarin canza kudi ta hanyar zuwa wurare irinsu Daura, Kurfi, Mani da Mashi."
"A yau jami'anmu sun fita duba sauran kananan hukumomin, musamman masu Naira Dubi Goma da abinda yayi kasa."
Naira: Ina sane da wahalar da talakawa ke sha, ban yi nufin tsananta musu ba
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira da yan Najeriya su kwantar da hankulansu game da lamarin sauya fasalin Naira da kuma wa'adin daina amfani da tsaffin takardun Naira.
Buhari ya ce zai tabbatar da cewa al'umma da kasuwancinsu basu wahala ba kuma kowa zai samu sabbin kudi cikin 'kankanin lokaci.
Asali: Legit.ng