Yan Najeriya Sun Lika Bandir-Bandir Din Sabbin Kudi a Wajen Biki Ana Tsaka Da Neman Su a Gari
- Wani bidiyo da ke yawo ya nuno yan Najeriya suna lika sabbin kudin da CBN ya buga a wajen biki
- Wani bidiyo da aka wallafa a Twitter ya sa mutane da dama tofa albarkacin bakunansu kasancewar mutane da yawa basu ga kudin ba a hannunsu
- Babban bankin Najeriya ya ce lallai a ranar 31 ga watan Janairun 2023 za a daina amfani da tsoffin kudi
Yayin da yan Najeriya ke ta zaryan zuwa ATM a fadin kasar saboda karancin sabbin kudade, bidiyoyin da aka wallafa a soshiyal midiya ya nuna yadda ake lika sabbin kudade a wajen wani biki.
Bidiyo ya nuno yadda mutane da dama ke nuna halin ko in kula da yanayin da yan Najeriya ke ciki yayin da suke fafutukar ganin sun mallaki sabbin kudade kasancewar wa'adin 31 ga watan Janairu da CBN ya gindaya na kara gabatowa.
Bankuna sun sha kwana da kudaden saboda kwastamominsu
Wani rahoton Ripples Nigeria ya bayyana cewa bankuna na da manyan kwastamomi wadanda ke yin kwana da sabbin kudade saboda sun fi basu fifiko.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Har ila yau, masu hada-hadar kudi na ta biyan karin kudi don cire makudan kudade na sabbin naira.
ATM din bankuna da dama basu da kudade a cikinsu yayin da ake samun cunkoson jama'a a wuraren da ke da tsabar kudi.
Babban bankin Najeriya ya nace cewa akwai isasun sabbin kudi a bankuna da zai kewaye koina yayin da bankuna kuma suka ce basu da kudi.
Yan Najeriya sun nemi a kara wa'adin
Duk rokon yan Najeriya da yan siyasa na ganin CBN ya kara wa'adin da ya bayar ya ci tura yayin da bankin ya ce wa'adin na nan daram-dam.
Bidiyon ya fusata jama'a
Bidiyon wanda @madona1996 ya wallafa a Twitter ya fusata yan Najeriya da dama.
@Emmalex_8 ya ce:
"Kuma bandir-bandir mutumin ya ke ta likawa faaaa, ya kamata a kama wanda ke lika kudin sannan a tambaye shi ya aka yi ya samu da yawa haka yayin da mutane basu gani ko rike shi ba; jiya ne sabon kudin ya shiga hannuna kuma na kashe shi."
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi kira ga babban bankin kasa a kan ya kara wa'adin daina amfani da tsoffin kudi a kasar saboda abun zai fi shafar mutanen karkara ne.
Asali: Legit.ng