Babban Malamin Addinin Kirista Ya Fada Wa Yan Najeriya Irin Yan Takarar Da Ya Kamata Su Kauracewa

Babban Malamin Addinin Kirista Ya Fada Wa Yan Najeriya Irin Yan Takarar Da Ya Kamata Su Kauracewa

  • Wani malamin addinin kirista ya bayyana cewa dole yan Najeriya su natsu su zabi shugaba na gari a 2023
  • Malamin yace bazai yi wu ayi ta addu'a kuma lokacin zabe a zabi shugabannin da suke da shaidar laifi ba
  • Ya bayyana cewa rashin shugabanci nagari yana maida Najeriya baya ya kuma hanata kaiwa inda ya kamata

Ogun - Babban malamin darikar Katolika na Ondo, Rabaran Jude Arogudale, ya yi kira ga yan Najeriya da su kauracewa yan takarar da ya kira ''sanannun masu laifi'' ne wanda hukumomin kasar sun tuhume su idan za su kada kuri'a.

Ya yi kiran ne yayin da yake gabatar da hudubar bikin cika shekara 25 da kafa Cocin Katolika ta Abeokuta, Jihar Ogun, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Sabbin Kudi: Mutanen Karkara Wa'adin CBN Zai Wa Illa, El-Rufai

Zabe a Najeriya
Babban Malamin Addinin Kirista Ya Fada Wa Yan Najeriya Irin Yan Takarar Da Ya Kamata Su Kauracewa. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Malamin addinin yace akwai bukatar a ceto Najeriya daga halin matsin da take wanda dole sai anyi hakuri an kawar da shugabannin da suke sayar da jin dadin yan kasa don amfanin kansu.

Arogundade ya shawarci yan Najeriya da zabi shugabannin da ke da nutsuwa da kuma shaidar kirki don ceto kasar nan daga karasa lalacewa.

Ya bayyana cewa Najeriya na karkashin kulawar ''masu zuciyar rashawa wanda suke siyar da jindadin yan kasa don darewa karagar mulki da kuma juya talakawa''.

Arogundade ya ce, abin bakin ciki ne, yadda tasirin addinin Kiristanci yaki bayyana saboda lalacewar shugabanci; rikicin kabilanci da kuma karuwar rashin mabiya addini.

A kalamansa:

''Bamu bane dai Yarabawa, Ibo, Hausa kuma yan kasar da muke rokon Ubangiji ya shiga lamarinmu ya magance mana yan siyasa masu cin hanci da rashawa kuma mu zo mu zabi yan takarar da aka tabbatar masu laifi ne a hukumomin kasashe ba?

Kara karanta wannan

'Kana Bukatar Taimako', Martanin Fadar Shugaban Kasa Ga Kalaman Tanko Yakasai Kan Tinubu

"Gaba dayanmu Kiristoci da wanda ba kiristoci ba muna neman shugabanci na gari wanda zasu saita mana kasar nan kamar yadda Allah yayi ta.
''To mu zabi na gari, mu ceto Cocin daga kuncin rashin zaben jagora na gari wanda zai wofantar da bukatunmu saboda bukatunsa."

Ya cigaba da cewa:

''Ya kamata alummarmu su fara tunani da kuma neman dan kishin kasa a cikinmu don gudanar da mulkin kasa da kuma gyara kura-kuren da akayi a shekarun baya.
''Ba zai yiwu mu zuba ido muna kallon kasarmu mai daraja ta durkushe sakamakon rikicin shugabanci da baya karewa ba, yana dawo da burin kasar da kuma hana kaiwa gaci''.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164