Yan Ta'adda Sun Kaiwa Dan Takarar Gwamnan Jihar Lagos Na Jam'iyyar PDP Hari
- An kaiwa jerin ganon kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar Lagos na jam'iyyar PDP, wanda wasu yan ta'adda sukai
- Manema labarai sun ce yan ta'addan sun jefe jerin ganon da muggan makamai ga yan kwamitin nasu
- An ce yan ta'addan sun hana dan takarar Abdul-aziz Adediran shiga wasu gurabe a jihar dan hana shi yin yakin neman zabe
Lagos - Wasu yan ta'adda sun kaiwa kwamitin yakin neman dan takarar gwamnan jihar Lagos hari a jiya laraba 25 ga watan Janairu a yankin Ikosi-Isheri dake kramara hukumar Kosefe.
Jaridar PMNewsNIgeria ta rawaito cewa an kaiwa kwamitin yakin neman zaben hari akan titin Oworo, da yake a yankin Oworosonki
Sun fara jifansa da da duwatsu, da kwalabe da kuma wasu abubuwa masu hatsari, sannan suka hana kwamitin shiga inda yake son shiga dan yakin neman zaben
An rawaito cewa dan takarar gwamnan ya hana jami'an tsaronsa da su harbi ko daki kowa, sabida abin zai iya kawo hautsini.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma jami'an tsaro sun sami nasarar tarwatsa, yan ta'addan, sannan suka tsare dan takarar har tsawon mintuna 45 dan tabbatar da komai ya lafa kafin su sakeshi.
Zaku iya kallon bidiyon anan
Jam'iyyar PDPn jihar Lagos tayi Allah wadai da kai harin jihar Lagos
A yayin da yake maida magana kan abinda ya faru, mai magana da yawun jam'iyyar PDP, na jihar Lagos, Hakeem Amode, ya yi Allah wadai da wannan abunda ya faru yana mai cewa wannan yiwa dimukuradiyya karan tsaye ne.
Amode ya roki shugaba Muhammadu Buhari da shugaban rundunar yan sandan kasa Usman Alkali Baba kan su binciki lamarin tare da samo bakin zaren abinda ya faru tare da daukar matakin da bazai kara faruwa ba.
Yayin da yake magana kan yakin neman zaben, Amode yace hukumar zaben Nigeria INEC ta bawa duk jam'iyyar da tai rijista da ita damar gudanar da yakin neman zabenta ba tare da hayaniya ko cin mutunci ba.
Ba'a kyauta mana ba
Mai magana da yawun jam'iyyar ya ce:
"Wannan wani abu ne wanda bazamu yarda da shi ba, ace jihar da ke ikirarin jihar da dake da martaba da kima amma a ringa irin wannan abun, kamata yayi ace an zabe lami lafiya"
Dokar zabe ta bada damar kowa yai yakin neman zabe a ko'ina a jihar nan tamu ta Lagos, ba tare da an hanamu ba, dan haka muke sanar da hukumomi da jam'a kan rashin kyautamana da akai, inji mai magana da yawun jam'iyyar
"Dan haka ina kira da shugaba Muhammadu Buhari, da yayi wa yan Nigeria alkawrin gudanar da sahihin zabe da ya tabbatar da hakan a jihar mu ta Lagos."
Daga karshe Hakeem yayi kira da shugaban rundunar yan sanda da sauran hukumomin tsaron kasar nan irin su DSS da su dau matakin da ya dace dan magance irin wannan abubuwan da suke faruwa
Asali: Legit.ng