Buhari Ya Bude Cibiyar Yadawa da Kiyaye Al’adu da Tarihin Yarabawa a Jihar Legas
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wata cibiya ta yada al’adun Yarbawa a jihar Legas
- Buhari ya kai ziyara jihar ta Legas ne domin kaddamar da ayyukan da gwamna Sanwo-Olu ya yi a jihar
- Shugaban na ci gaba da yawo a jihohin kasar nan don yin kamfen na APC da kuma kaddamar da ayyuka
Jihar Legas - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da cibiyar John Randle ta kiyayewa da yada al’adu da tarihin Yarbawa a jihar Legas.
Shugaban ya kaddamar da aikin ne a ranar Talata 24 ga watan Janairu yayin wata ziyara a jihar, jaridar Punch ta ruwaito.
A lokacin kaddamarwar, Buhari yana tare da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwushi da dai sauran jiga-jigan yankin.
Idan baku manta ba shugaba Buhari ya kai ziyara jihar Legas domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin APC ta Sanwo-Olu ta yiwa jihar.
Ya kasance a jihar Legas tun ranar Litinin 23 ga watan Janairu jim kadan bayan kammala gangamin kamfen na APC a jihar Bauchi.
Martanin jama’a a Twitter
Bayan da jaridar ta yada bidiyon shugaban a jihar Legas lokacin da yake kaddamar da aikin, mutane da yawa sun yi matani. Ga kadan daga ciki:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
@RabiuMo43358460
“Allah ya yi albarka Baba Buhari.”
@Letsgonow10
“Wannan abu namu ne (Yarbawa), amma abin haushi Bafulatani ne mai bude shi.”
@_Konrade
“Yarbawa sun kare gobensu, kuma za su iya yin alfahari da hakan. Shugabanninsu, duk da bambancinsu, kansu a hade yake.”
@teewesthojo
“Shin cewa kuka yi tarihi ko salsala?”
Buhari zai kaddamar da jirgin da aka kera a Najeriya kafin ya sauka a mulki
A wani labarin kuma, kunji yadda wata hukuma a Najeriya ta bayyana cewa, shugaba Buhari zai kaddamar da wani jirgin sama mai sauakr ungulu da aka kera a Najeriya.
A cewar hukumar, an dauki lokaci ana wannan aikin mai muhimmanci kuma ana sa ran shugaban ne zai kaddamar dashi nan da zuwa lokacin da zai sauka.
Ba wannan ne karon farko da ake kirkirar kayayakin fasaha ba a Najeriya, an sha yin hakan a baya, kuma ana samun nasara su haifar da mai ido.
Asali: Legit.ng