Jihar Katsina Ta Ware Ranakun Alhamis Da Juma'a Dan Yiwa Buhari Barka Da Zuwa Jihar

Jihar Katsina Ta Ware Ranakun Alhamis Da Juma'a Dan Yiwa Buhari Barka Da Zuwa Jihar

  • Bayan kaddamar da aiyuka a jihar Lagos, shugaba Buhari zai kaddamnar da wasu aiyukan a jiharsa ta katsina
  • Gwamnatin jihar ta katsina ta ware wasu kwanaki dan tarbar shugaba Buharin sabida jama'ar jihar Katsina su samu dama tarar sa
  • Gwamnatocin jihohi dai na ta kokarin kwammala aiyukan da suke ganin manya ne kafi lokacin babban zaben 2023

Katsina - Jihar Katsina ta ayyana ranar Alhamis 26 da Juma'a 27 ga watan Janairun nan, a matsayin ranakun da ba aiki, dan yiwa shugaba Muhammadu Buhari maraba da zuwa jihar.

Gwamnati tace ta bada hutun ne, dan shugabanni da wanda suke kananan hukumomin wajen Ktsina shigowa dan tarbar shugaba Buhari.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da sakataren dindin na ma'aikatar kula da labarai da al'adu na jihar Alh Sani Bala Kabomo ya sanyawa hannu a yau.

Kara karanta wannan

Kano: Buhari Zai Kai Ziyarar Kwanaki 2, Zai Kaddamar da Wasu Manyan Ayyukan Ganduje

Ana sa ran shugaba Buhari zai isa jihar Katsina dan akddamar da wasu aiyukan raya kasa da gwamnatin jihar Katsina tayi a karkashin gwamna jihar Aminu Bello Masari. Rahoton ThisDay

Ziyarar Buhari
Jihar Katsina Ta Ware Ranakun Alhamis Da Juma'a Dan Yiwa Buhari Barka Da Zuwa Jihar Hoto: Vanguard
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dalilin Ziyarar

PMNewsNigeria ta rawaito dalilin ziyarar Buharin shine sanarwar da ta bayyana dalilin da shugaba Buharin zai kai ziyarci jihar tasa ta katsina a ranakun Alhamis da Juma'a din.

Sakataran ma'aikatar labarai da al'adu na jihar ya karantawa sanarwar kamar haka:

"Mun bada wannan hurun ne, dan yiwa shugaba muhammadu buhari barka da zuwa jiharsa ta haihuwa kuma jihar mu ta katsina, domin kaddamar da wasu aiyukan raya kasa wanda gwamnan jihar nan yayi"

Ya ci gaba da ce:

"Makasudin hakan shine wanda suke a kananan hukumomin wajen katsina su sami damar shigowa cikin gari dan tarbar shugaban.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Bayan Gazawar APC da PDP, Yan Najeriya Suna da Wani Zabi Ɗaya Rak

Sanarwar tace wannan hutun bai shafi ma'aikatan gwamnatin tarayya ba, bankuna da kuma ma'aikatun da suke da gaggawa

Alh Bala Kaboma yace:

"muna kira ma'aikata da jam'ar gari da su fito kwansu da kwarkwatarsu, suyi dafifi dan tayarr shugaba buhari wanda zaizo da yan tawagarsa bude aiyukan alheri"

Buhari ya kaddamar da aiyuka a jihar Lagos

A jiya ne shugaba buhari ya kaddmar da wasu aiyuka a jihar Lagos lokacin da ya ziyarci jihar na kwana biyu.

Daga cikin abubuwan da Buharin ya kaddamar akwai tashohin jirgin kasan cikin gari, da tashar bakin ruwa da kuma kamfanin sarrafa shinka.

Sauran sun hada da cibiyar kula da al'adun yarabawa da kuma wasu kananun aiyukan da jihar Lagos tayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida