Wajibi Ne A Kara Wa'adin Daina Amfani Da Tsaffin Naira Zuwa Watan Yuli: Majalisar Dattawa Tayi Ittifaki

Wajibi Ne A Kara Wa'adin Daina Amfani Da Tsaffin Naira Zuwa Watan Yuli: Majalisar Dattawa Tayi Ittifaki

  • Majalisar dattawa ta mayarwa gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, martani
  • Sanatocin sun kada kuri'ar jin ra'ayi kan dage wa'adin ranar 31 ga Junairu da bankin CBN ya sanya
  • Saura kwanaki bakwai kacal wannan wa'adi ya cika kuma yan Najeriya sun ce da sauran rina a kaba

Abuja - Mambobin Majalisar dattawan Najeriya wadanda aka fi sani da Sanatoci sun bayyana cewa wajibi ne a dage ranar daina amfani da tsafiin takardun Naira da watanni shida.

Sanatocin a zaman da tayi ranar Talata, 24 ga Junairu, 2023 sun yi ittifaki bayan kada kuri'a cewa a dage wa'adin daina amfani da tsaffin kudin daga ranar 31 ga Junairu zuwa 31 ga Yuli, 2023.

Naira
Wajibi Ne A Kara Wa'adin Daina Amfani Da Tsaffin Naira Zuwa Watan Yuli: Majalisar Dattawa Tayi Ittifaki
Asali: Getty Images

Wannan ya biyo bayan kudirin da Sanata Sadiq Umar mai wakiltan Kwara ta Arewa ya gabatar a zauren majalisa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bamu Yi Umurnin Mayar Da Tsaffin N1000 da N500 Kowani Banki Ba, CBN

Hakazalika kuma Sanata Ali Ndume, ya nuna goyon bayansa ga kudirin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanata Sadiq ya ce akwai bukatar bankin ya jinkirta daina amfani da kudin sai sabbin kudaden sun yawaita cikin al'umma.

A baya majalisar ta roki babban bankin Najeriya CBN ya dage wa'adin zuwa karshen watan Yuni, 2023.

Ba zamu dage wa'adi ba

Gwamnan CBN a ranar Talata ya bayyana cewa sam basu da niyyar dage wa'adin daina amfani da tsaffin takardun Naira.

Godwin Emefiel ya bayyana cewa kwanaki 100 da aka bada sun isa kowa ya mayar da kudinsa banki.

Saura kwanaki bakwai wa'adin 31 ga Junairu

Kawo yau 24 ga watan Juaniru, 2023, yan Najeriya da dama sun bayyana cewa har yanzu bankuna ba bada tsaffin kudade maimakon sabbi.

Legit ta tattara ra'ayoyi wasu daidaikun yan Najeriya inda suka bayyana ra'ayoyinsu game da lamarin daina amfani da tsaffin kudi.

Kara karanta wannan

Dalilai 5 Da Yasa Muka Kawo Tsarin Sauya Fasalin Naira: Buhari Da Safiyar Yau

Rislanu Shehu Kibiya yace:

Allah yasa hakan yaxama Alkhairi agaremu baki daya Amma dai abin babu dadi domin Al'umma suna chikin wani hali

Aminu Liman Yala yace:

Kar amanta' yanda muke haka ake turomana shugabanni dai daidamu, donhaka adaina tsine musu, kowa yayi hisabi wa kansa' allah kashiryemu.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida