Kai Tsaye: Yadda Taron Kamfen APC Ke Gudana Yau A Jihar Bauchin Yakubu

Kai Tsaye: Yadda Taron Kamfen APC Ke Gudana Yau A Jihar Bauchin Yakubu

Jirgin yakin neman kujerar shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 na jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress APC ya garzaya jihar Bauchin Yakubu, Arewa maso yammacin Najeriya a yau Litnin, 23 ga watan Junairu, 2023.

Mun kawo muku rahoton cewa shugaba Muhammadu Buhari ne zai jagoranci kaddamar da kamfen dan takaran shugaban kasa da gwamnan jihar Bauchi.

Dan takarar shugaban kasan APC, Bola Tinubu; abokin tafiyarsa, Kashim Shettima; Shugaban uwar jam'iyyar, Adamu Aliyu da sauran jiga-jigai sun dira Bauchi.

Jawabin dan takarar gwamnan jihar Bauchi karkashin APC

Dan takarar gwamnan jihar Bauchi karkashin APC, Air Marshal Abubakar Sadique, ya bayyana cewa shekaru biyar da yayi yana aiki da Buhari matsayin shugaban hafsun sojin sama, ya bashi kwarewa wajen mulki.

Ya yi alkawarin cewa idan al'ummar Bauchi suka zabesa, zai yi adalci kuma zai inganta ilimi..

Ya bayyana cewa sama da jihohin Arewa shida aka bude rundunar mayakan sama karkashin mulkin shugaba Buhari.

Jihohin da ya lissafa sun hada da Birnin gwari a Kaduna, Bauchi, Agatu a Benue, dss.

Yace;

"Zamu koma da yara miliyoyi makaranta, zamu tabbatar da mun taimaki matasa. Insha Allahu zamu tabbatar da cewa mun fitar da asibitoci masu aiki don taimakawa jama'a."
"Game da arzikin mai kuwa, muna kira ga jama'ar Bauchi su zabi Tinubu da yan takarar APC da su cigaba da wannan kokari."

Muna iya ci da kanmu saboda kokarin Buhari

Gwamna Atiku Bagudu ya bayyana cewa sakamakon irin kokarin da shugaba Buhari yayi a shekaru bakwai da suka gabata, Najeriya ta baiwa yan adawa kunya.

Bagudu ya ce yanzu Najeriya na iya ci da kanta ba tare da shigo da kayayyaki daga kasashen waje.

Bagudu
Kai Tsaye: Yadda Taron Kamfen APC Ke Gudana Yau A Jihar Bauchin Yakubu
Asali: UGC

Gwamnoni 6 kacal suka halarta a Bauchi

A madadin gwamnonin jam'iyyar APC, gwamnoni takwas suka halarce a taron kamfen Tinubu/Shettima a jihar Bauchi.

Gwamnonin sun hada da gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong; gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum; Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa, da gwamnan jihar Jigawa, Badaru Talamiz.

Dubban mutane yayinda Buhari ya isa filin taron Tafawa Balewa

Yanzu Shugaba Buhari ya isa filin kwallon tunawa da Sir Abubakar Tafawa Balewa, domin bude da taron kamfen Tinubu/Shettima da kuma Air Marshal Abubakar Sadique.

Shugaba Buhari ya dira Bauchi

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira jihar Bauchi da safiyar nan domin bude taron kamfen yakin neman shugaban kasa da kuma daga hannun dan takaran gwamnan jihar.

Cikin abin mamaki, shugaba Buhari ya samu kyakkyawan tarba daga wajen gwamnan jihar Bauchi kuam dan takarar kujerar gwamnan jihar, Bala Abdulkadir wanda aka fi sani da Kauran Bauchi.

BUhari
Kai Tsaye: Yadda Taron Kamfen APC Ke Gudana Yau A Jihar Bauchin Yakubu
Asali: Twitter

Online view pixel