Fasinjojin Jirgin Kasa Sun Shiga Tsaka Mai Wuya, Jirgi ya Tsaya Tsakiyar Dajin Kogi
- Wani jirgin kasa da ya taso daga Warri zuwa Itakpe ya lalace a tsakiyar dokar daji, wanda hakan ya jefa tsoro a zukatan fasinjojin da ya debo
- An ruwaito yadda lamarin ya auku karfe 12:00 na rana bayan tasowar jirgin kasa da kilomita 20 a safiyar Lahadi, wanda hakan yasa NRC nemo motocin kwashe fasinjojin
- Sai dai, kawo izuwa yanzu, babu wanda ya san sanadiyyar lalacewar jirgin kasan sannan babu wanda ya samu rauni
Wani jirgin kasa da ya tashi daga Warri zuwa Itakpe ya lalace, hakan ya tilasta fasinjoji sagalewa kan hanya. An tattaro yadda lamarin ya auku a dajin Kogi.
Fasinjoji da dama sun yi watsi da jirgin kasan saboda tsoron kada a yi garkuwa da su.
An gano yadda jirgin ya taso daga Warri a safiyar Lahadi, amma ya lalace misalin karfe 12:00 na rana cikin dajin da ke tsakanin Ajaokuta da Itakpe.
2023: Ka Janye Idan Ka San Ba Ka Da Lafiya, Malamin Addini Ya Gargadi Yan Siyasa, Ya Ce Wani Jigo Zai Mutu
Rundunar 'yan sandan jihar Delta da na jihar Kogi basu tabbatar da aukuwar lamarin nan take ba, sai dai, Manajan titin jirgin kasa Warri zuwa Itakpe ya shaidawa wakilin The Punch yadda ya ke kan hanyarsa na zuwa wurin gami da alkawarin bada cikakken bayani daga bisani.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kamar yadda wani daga cikin ma'aikatan hukumar jirgin kasan na tashar Itakpe ya bayyana, lamarin ya auku kimanin kilomita 20 daga inda ya taso.
Majiyar ta kara da bayyana yadda wasu daga cikin ma'aikatan NRC suka nemo motoci don kwashe fasinjojin daga dajin da lamarin ya auku.
"Wurin bai da nisa daga tashar mota, saboda haka wasu daga cikin ma'aikatanmu sumnkira motar kabo-kabo daga tashar a Itakpe don kwashe duk fasinjojin.
"Bai da nisa kawai kilomita 20 zuwa inda lamarin ya auku. Babu wanda ya samu rauni."
Jama'a Sun Yabawa Kwandastan Motan da ya Dire daga Bas, Ya Tafi Nemawa Fasinja Mara Lafiya Ruwan Sha
- Ya shaidawa The Punch.
Yayin jawabi game da abun da ya janyo lalacewar jirgin kasan, ya ce:
"Har yanzu ba zamu iya cewa ga abun da janyo hakan ba, injiniyanmu ya je wurin don dubawa, sai dai kawai abun tuka jirgin ne ya dakata da tafiya."
Yayin tabbatar da aukuwar lamarin, wata majiya a NRC ta ce:
"Yau ne da safe, a tashar Kogi, tasha ce inda fasinjoji basa tsayawa; sun rufe tashar. Kamar dai wani ya lalata dogon, yayin da jirgin ya isa wurin, ya daina aiki; kusan tayoyi hudu na jirgin sun lalace; sun kusa gabza hatsari."
Hukumar kidaya ta sanar da ranar fara kidayar 2023
A wani labari na daban, Hukumar Kidaya ta kasa ta sanar da cewa za a fara kidayar jama'a gidaje a watan Maris zuwa Afirilu.
Asali: Legit.ng