Yan Sanda Sun Kama Matasa 33 Kan Kisan Dagacin Lambata a Jihar Neja
- Rundunar yan sanda a jihar Neja ta cika hannu da wasu matasa 33 da ake zargi da aikata laifuka
- An kama matasa 14 kan kisan gagacin Lambata yayin da sauran 19 aka kama su kan kona ofishin yan sanda a Kaffin-Koro
- Wasu fusatattun matasa ne suka sassare basaraken, Alhaji Mohammed Abdulsafur da kaninsa makonni biyu da suka gabata
Niger - Rundunar yan sanda a jihar Neja ta kama mutum 33 da ake zargi a kan kisan dagacin Lambata, Alhaji Mohammed Abdulsafur, da kona wani ofishin yan sanda, jaridar Vanguard ta rahoto.
An kama matasa da ake zargi da kisan dagaci yayin binciken gida-gida
An tattaro cewa 14 daga cikin fusatattun matasan sun farmaki gidan dagacin makonni biyu da suka gabata sannan suka ji masa mummunan rauni da kaninsa, Ibrahim Mohammed.
Gwamnan Barno Yakoka Kan Yadda Sabbin Kudin Da CBN, Ya Shigo Dasu Basa Zagayawa A Tsakanin Al'ummarsa
Yayin da aka tabbatar da mutuwar dagacin kauyen daga bisani a asibiti, kaninsa ya tsira da munanan rauni.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jami'an yan sanda da suka shiga aiki nan take don gano musababbin rikicin karkashin jagorancin kwamandan Suleja sun bi gida-gida don bincike inda a nan ne suka kama wasu daga cikin wadanda ake zargin.
Wata sanarwa daga kakakin rundunar yan sandan, DSP Wasiu Abiodun, ya ce wadanda ake zargin sun yi jawabin fallasa kan lamarin.
Matasan da ake zargi da kona ofishin yan sandan Kaffin-Koro sun shiga hannu
An kuma kama wasu 19 kan kona ofishin yan sandan Kafin-Koro yayin zanga-zanga a kan kisan Rabaran Isaac Achi, rahoton Leadership.
Rundunar yan sandan ta ce:
"Yayin zanga-zangar, matasan sun hada kai a tsakaninsu sannan suka farmaki hedkwatar yan sanda ta Kaffin-Koro da muggan makamai kamar su sanduna, duwatsu, kwalabe, da fetur da sauran makamai, sannan a lokacin da yan sandan ke kokarin basu kariya a zanga-zangar lumanan da suke yi, matasan sun aiwatar da ta'asarsu sannan suka cinnawa hedkwatar wuta inda motoci hudu da babura goma suka kone ciki harda muhimman takardu.
Yayin bincike, shugaban fusatattun matasan ya bayyana dukkanin wadanda ake zargi da hannu wajen aikata ta'asar, sannan ya kuma ambaci kimanin wasu 28 wadanda a yanzu haka suka gudu."
Magajin garinb Lambata ya kwanta dama
Mun kawo a baya cewa Magajin Garin Lambata, Mohammed Abdulsafur, mutu sanadiyar wani rikici da ya barke tsakanin matasa.
Mun dai ji cewa Abdulsafur ya mutu ne sakamakon raunukan da ya matasan suka masa yayin harin.
Asali: Legit.ng