Dole INEC Ta Dage Zaben 2023 Zuwa Wani Lokacin, Malamin Coci, Ayodele Fadi Dalilai
- Babban malamin coci a Najeriya ya ce akwai bukatar a sake fasalin abubuwa da yawa a Najeriya don kawo ci gaba
- Ya kuma ce akwai bukatar INEC ta dage zaben 2023 saboda akwai wadanda ke shirin kawo tsaiko ga zaben a wasu wurare
- ‘Yan Najeriya na ci gaba da nuna damuwa game da faruwar zaben 2023, INEC da hukumomi sun ce za a yi zabe babu gudu babu ja da baya
Najeriya - Babban shugaban INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele ya gargadi hukumar zabe ta INEC da ta gaggauta dage zaben 2023 da ke tafe nan da kwanaki don gujewa matsala.
Wannan na fitowa ne daga cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun hadiminsa, Osho Oluwatosin, wanda jaridar Tribune ta samo.
Primate ya ce, ba zai yiwu a yi zabe a wasu yankunan kasar nan ba saboda idan aka yi shi a lokacin da aka tsara, akwai wadanda za su yiwa wasu rumfunan zabe barin makauniya.
Ya bayyana cewa, idan INEC tana son samun nasara, to tabbas dole ta dage zaben don sake yin kyakkyawan shiri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa:
“Idan INEC bata daga babban zaben nan ba, ba za a yi shi a wasu wurin ba kuma hakan zai kai samun sakamako mai gibi. Akwai wadanda za su yi cin dunduniya ga zaben a wasu wurare.”
Mafita ga matsalolin Najeriya
Hakazalika, Primate ya bayyana cewa, mafita ga dukkan matsalolin Najeriya ba komai face sake fasali, ba wai zabe na.
Ya ce matukar ba a samu tsarin gyara mai kyau ba, kasar za ta iya rugujewa a kowane lokaci daga yanzu, rahoton Punch
Game da hadin kai a Najeriya, ya ce idan aka sake fasalin abubuwa a kasar, hakan zai kawo ci gaba ya kuma hada kan ‘yan kasar.
A cewarsa, maganganun da ya fada na gyaran Najeriya Allah ne ya sanar dashi, kuma ya kamata a dauka cikin gaggawa.
Ganawar shugaban INEC da shugabannin jam'iyyu
Yayin da ake ci gaba da jiran zaben 2023, hukumar zabe ta zauna da jiga-jigai kuma shugabannin jam'iyyun siyasar kasar nan.
A ganawar, an ce an bayyanawa shugabannin adadin masu kada kuri'u da kuma katunan zaben da suka rage ba a karba ba.
Hukumar ta kuma ba da tabbacin za a yi zaben 2023 ba tare da wani tsaiko ko matsala ba.
Asali: Legit.ng