Dan Najeriya Ya Tarawa Wata Tsohuwa Tallafin Kudi a Kafar TikTok, Ya Kai Mata N1m Har Gida
- Wani dan Najeriya ya gamu da wata tsohuwa sai ya yanke shawarin ya nishadantar da ita ba wai ta tika rawa kadai ba, ya bata kyautar kudi
- Dan rawan mai suna Bryt Iwundu ya ga stohuwar ne a zaune a titi, daga nan ya yi rawa a gabanta, bayan haka ya nemo ta ya ba ta kudi
- Mabiyansa a kafar TikTok sun shiga mamakin yadda ya dauki kudi N1,000,000 ya ba ta, jama’a sun yi martani mai daukar hanakli
Wata tsohuwa a Najeriya ta samu kyautar kunshin kudi N1m daga wani dan TikTok mai suna Bryt Iwundu.
Wannan na zuwa ne bayan da Bryt ya gamu da tsohuwar a bakin titi tana zaune, ta yi rawa a gabanta don nishadantar da ita. Murmushin da ta yi a lokacin ya nuna ta jiku da rayuwar.
Bai tsaya a nan ba, ya tattara mabiyansa domin tarawa wannan matar kudi, inda ya tara kudade masu yawan ban mamaki.
Bidiyon tsohuwar da aka tarawa tallafin miliyan 1 ya bazu
A wani bidiyon da ya yada, ya bayyana ncewa, ya bi matar har zuwa gidanta domin gano inda take rayuwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce mutane da yawa sun masa magana a TikTokm cewa suna son tallafa mata da kudi idan zai yiwu.
Daga nan ne ya karo-karon kudaden daga mutane da yawa, ya tara N1m domin ba wannan baiwar Allah.
Wani yanayi mai cike da kawazuci lokacin da matar ta karbi kyautar da aka tattara mata daga jama’a,
Jama’ar yanar gizo sun yabawa Bryt bisa wannan aiki karimci, sun masa addu’o’in ci gaba.
Kalli bidiyon da ya yada:
Martanin jama’a
Ga kadan daga abin da mutane ke cewa game da wannan karimci:
@Clinton Rex yace:
"Allah ya yi albarka. Bana tsammanin mama ta ji an ce 1m da kyau.”
@user6859896268161 yace:
"Allah ya yi maka albarka. Kamar babu kawa-zuci a idon matar.”
@sandratitilayo.12 yace:
"Ya kamata ka bata kudin ne mutane suna gani."
@khalixta21 yace:
“Allah ya yi maka albarka bisa wannan aikin mai kyau.”
Kudin Bogi Na Yawo, Mai POS Ya Ba Wani N1,000, Ya Gano Matsala Bayan Kwanaki
A wani labarin kuma, kunji yadda wasu mutane suka ba dan jarida a Najeriya kudin bogi, ya yi kira da cewa ya kamata a kula.
Wannan na zuwa ne bayan da aka sauya wasu daga cikin kudaden Najeriya domin magance matsalolin tsaro da na tattalin arziki.
Ali Ahmed Geidam ya bayyana yadda mai sana'ar POS ya ba shi kudin da ba na gaske ba, an ki karba a jiharsa.
Asali: Legit.ng