Kotu Ta Daure Dagaci Kan Kin Biyan Bashin Wanda Ya Ranta Masa Kudi Ya 'Siya' Sarauta A Adamawa
- Kotu ta yanke wa dagajin kauye hukuncin daurin shekaru takwas a gidan gyaran hali a jihar Adamawa
- Sunaka, wanda ya shigar da kara a kotun ya ce Gumni Ilihu ya karbi tumakinsa 13 ya siyar don ya samu sarauta
- Amma bayan Ilihu ya samu sarautan sai ya ki biyan Sunaka kudinsa har ma ya yi barazanar zai kore shi daga garin
Adamawa - Kotun majistare a jihar Adamawa yanke wa wani dagajin kauye, Gumni Ilihu, na kauyen Gugu, yankin Banjiram a karamar hukumar Guyuk daurin shekara takwas a gidan yari saboda cin amana, makirci da firgitarwa.
Wani malamin firamari mai suna Roel Sunaka, dan shekara 47, ya kai Ilihu kara a kotu kan rashin biyansa tumaki 13 da ya sayarwa dagajin, rahoton The Punch.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sunaka, wanda supervisor ne a makarantar firamare ta Bobini a karamar hukumar Guyuk, ya ce bayan ilihu ya yi amfani da kudin da ya sayar da tumakin ya samu sarauta, ya ki biyansa kuma ya fara masa barazana cewa zai kore shi daga garin.
Yayin da ya ke yanke hukunci, Hyellamada Hyellandendu ya samu wanda aka yi karar da laifin cin amana.
Hyellandendu ya ce:
"Saboda cin amana, kai Cif Gumni Ilihu, an yanke maka daurin shekaru biyar da zabin biyan tara ta N100,000, daurin shekara guda saboda barazana da zabin tarar N25,000, sai daurin shekaru biyu na makirci da zabin biyan tara na N50,000."
Alkalin kotun ya ce wanda aka yanke wa hukuncin zai yi zaman gidan yarin a gwamutse.
Ya yi barazanar kora ta daga kauyen mu idan na ciagaba da tambayarsa kudi na, Sunaka
Da ya ke magana da yan jarida kan shari'a, Sunaka ya ce:
"Na tafi kotu saboda shi Gumni (Ilihu) ya sayar da tumaki na 13 a 2013 ya yi amfani da kudin ya nemi sarauta a matsayin dagaci wato Sarki Gugu. Na yi kokarin nema ya biya ni amma ya ki.
"Sau da yawa, bayan ya zama dagaci, ya yi barazanar sai kore ni daga kauyen idan na cigaba damunsa ya biya ni kudin da na bashi."
Asali: Legit.ng