An Gurfanar Da Ma'aikatan Otel Kan Sace N900,000 Na Kwastoma Daga Motarsa
- Yan sanda a Jihar Benue sun gurfanar da wasu ma'aikatan otel a kotu kan zargin satar kudi
- Ana zargin mutane ukun ne da balle kofar wani kwastoma da ya kawo baki tare da sace N900,000
- Amma, ma'aikatan otel din da aka gurfanar a kotun sun musanta zargin kuma kotu ta bada belinsu
Benue - Rundunar yan sandan jihar Benue a ranar Laraba ta gurfanar da wani Fegha, dan shekara 40, Tersoo Ayen, dan shekara 32 da Bemdoo Igbahemba, dan shekara 29 a kotun majistare kan zargin hadin baki, makirci da sata.
Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeta Kwegh Abugh, ya fada wa kotu cewa wani Tarnongo Tiza, ma'aikacin hukumar kula da ingancin kaya na Najeriya, ne ya kai korafi a hedkwatar yan sanda.
Abugh ya ce wanda ya kawo korafin ya ce ya sauke wasu bakinsa a otel din Trust Resort da ke lamba 3 Lucy Aluor Street, New GRA Makurdi ya ajiye motarsa a gaban ofis din mai bada daki ya shiga ciki.
Ya ce ofishin mai masaukin bakin na kusa da kofar shiga otel din inda za a iya ganin kyamara na CCTV.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mai shigar da karar ya ce:
"Yayin da ya fito daga ofishin mai masaukin baki, ya gano an bala gilashin gefen direba na sace masa N900,000."
Ya ce yayin binciken yan sanda sun kama Charles Fegha, Tersoo Ayen, da Bemdoo Igbahemba da sauran ma'aikatan otel din kan aikata laifin, rahoton The Punch.
Ya ce laifin ya saba da sashi na 97, 329 da 288 na Penal Code na dokar jihar Benue na 2004.
Abugh ya ce ana cigaba da bincike kuma a basu lokaci su kammala binciken.
Amma, da aka gurfanar da wadanda ake zargin, sun musunta aikata dukkan laifan.
Alkaliyar, Mrs Kadoom Gbasha, ta bada belin wadanda aka zargin kan N100,000 kowanensu tare da wanda zai karbe su da zai kasance ma'aikacin gwamnatin Benue.
Gbasha ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Fabrairu kamar yadda NAN ta rahoto.
An gurfanar da wani bawan Allah a kotu kan satar biskit na N1250 daga wani shago
A wani rahoton, an gurfanar da Sunday Hungbeji dan shekarar 31 gaban kotun majistare da ke zamansa a Badagry Legas kan satar biskit na N1250 samfurin shortbread.
Mutumin wanda ba a bayyana inda ya ke zaune ba, ana tuhumarsa ne da laifi guda daya tak na sata, rahoton Premium Times.
Asali: Legit.ng