Hukumar Shige da Fice Ta Najeriya Za Ta Dauki Ma’aikata, Abubuwa 12 da Ya Kamata Ku Sani

Hukumar Shige da Fice Ta Najeriya Za Ta Dauki Ma’aikata, Abubuwa 12 da Ya Kamata Ku Sani

A ranar Litinin 16 ga watan Janairu ne hukumar shige da fice ta Najeriya ta bude shafinta don daukar ma'aikata na 2023 a fadin kasar nan, jaridar Punch ta rahoto.

Kafar neman aiki a bude take ga duk mai sha'awar aiki da hukumar Civil Defence, hukumar gidan gyara hali, hukumar kashe gobara da kuma hukumar shige da fice ta kasa.

Jami'an hukumar shige da fice ta Najeriya
Hukumar Shige da Fice Ta Najeriya Za Ta Dauki Ma’aikata, Abubuwa 12 Ya Kamata Ku Sani Hoto: Punch
Asali: UGC

A wannan zauren mun tattaro wasu muhimman abubuwa 12 da ya kamata mutum ya sani don samun garabasar shiga wannan aiki, sune kamar haka:

1. Ranar da aka bude kwasar aikin da ranar da za a rufe

An bude kwasar aikin hukumar NIS a ranar Litinin, 16 ga watan Janairun 2023 kuma za a rufe bayan makonni biyu wanda ya yi daidai da 30 ga watan Janairu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Ba a Afrika kadai bane: Kamar dai na ASUU, malamai a Ingila za su shiga yajin aiki

2. Tsarin neman aikin

Za a yi duk wani cike-ciken neman aikin ne a yanar gizo kuma ana sa ran masu neman aikin za su shiga shafin su cike fom sannan su mika shi.

Ana shawartan masu neman aikin da su yi pirintin fam din wadanda za su tsaya masu wanda dole a cike sannan a gabatar da shi a yayin tantancewa.

3. Guraben da ake da su da kuma matakin karatun da ake bukata

Rukunin A: Superintedent Cadre:

i. Mukamin SI ana bukatar kwararrun likitoci: Dole wanda ke neman wannan matsayin ya mallaki digiri na farko a MBBS daga sanannen jami'a da kuma takardar shaidar kammala NYSC ko na dauke masa zuwa bautar kasa.

ii. Mukamin DSI ana bukatar kwarrun masana ilimin hada magunguna: Dole wanda zai nemi aikin ya mallaki digirin farko a bangaren hada magunguna daga sananniyar jami'a da takardar shaidar kammala NYSC ko na dauke masa zuwa bautar kasa.

Kara karanta wannan

Sharri aka min: Dan sandan da bindige lauya mai juna biyu ya musanta zargin kisa

iii. Mukamin ASI: Dole mai neman aikin ya mallaki digiri, HND ko madadinsu daga sananniyar makaranta.

Rukunin B: Inspectorate Cadre:

i. Mukamin AII: Dole mai neman aiki ya mallaki kwalin Difloma, NCE ko NABTEB daga sananniyar makaranta.

Rukunin C: Assistant Cadre:

i. Mukamin IA 111: Dole mutum ya mallaki kwalin GCE, SSCE/NECO ko madadinsu da akalla kiredit 4 a zama da bai wuci 2 ba, wanda dole a samu Turanci da ilimin Lissafi.

ii. Mukamin IA III: Aikin hannu: a) direban mota b) Bakanike: Dole mutum ya mallaki SSCE ko madadinsa da takardar gwajin sana'a da ya kamata.

3. Kasar mai neman aiki

Hukumar NIS ta ce dole mai neman aikin ya zama dan Najeriya.

4. Takardun da ake bukata don neman aikin

i. Takadar shaidar dan kasa

ii. Kwafin takardun kammala karatu da aka bukata a sama.

iii. Takardun gwajin lafiya daga sanannun asibitocin gwamnati.

5. Gwajin kwaya da sauransu

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Wasu sun dauko yara 41 daga Arewa, za su kaiwa fasto a Kudu, sun shiga hannu

Dole masu neman aiki su yi gwajin kyawa don daukarsu aiki.

6. Karfin aljihu

Koda dai hukumar NIS bata fadi matsayin kudin da mutum zai mallaka ba, ta ce dole mutum ya zama ba matsiyaci ba.

7. Yawan shekaru

Dole masu neman aikin sun kasance tsakanin shekaru 18 da 30 banda likitoci da masana ilimin hada magunguna wadanda aka ce kada su haura shekaru 35.

8. Ilimin kwamfuta

Koda dai wannan ba dole bane, NIS na ganin zai karawa mutum damar da yake da shi.

9. Fadin kirji

Wannan maza kadai ya shafa kuma dole su kasance basu yi kasa da 0.87 ba.

10. Rashin gabatar da takardun makaranta

NIS ta ce duk takardar da ba a nuna shi kuma aka amince da shi a yayin neman aiki ba, ba za a amince da shi ba bayan daukar aiki.

11. Rashin cancanta

NIS ta ce yan takarar da suka nemi aiki fiye da sau daya ba za a dauke shi ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: INEC Ta Tsawaita Lokacin Dena Bada Katin Zabe Na PVC Gabanin Zaben 2023

12. Tsarin jarrabawa

Tsarin jarrabawar daukar aiki da za a yi wa wadanda sunansu ya fiyo zai kasance kan na'ura kuma za a sanar da su lokaci da ranar da za a yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng