Jarumin Fim ya Burmawa Makwabci Wuka kan N1,000, An Gurfanar Dashi
- Wata kotun laifuka tana tuhumar wani jarumin wasan kwaikwayo, Temitayo Ogunbusola mai shekaru 30 da dabawa makwabcinsa Oladotun Osho makami har lahira
- An ruwaito yadda rikici ya barke tsakanin wanda ake tuhuma da marigayin kan kudin NEPA wanda shi da wasu daga cikin 'yan hayan gidan suke da matsala da shi
- Sai dai, ana tsaka da haka ne wanda ake tuhumar ya fada daki ya dauko wukar yanka albasa ya burmawa marigayin a kirji
Wani jami'in binciken 'yan sanda (IPO), Insp Israel Ojo, ya sanar da wata kotun laifuka yadda wani jarumin wasan kwaikwayo mai shekaru 30, Temitayo Ogunbusola, ya dabawa makwabcinsa, Oladotun Osho makami har lahira saboda N1,000 na kudin wutar lantarki.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito yadda ake tuhumar Ogunbusola da laifin kisan kai, wanda ya musanta.
Ojo ya sanarwa kotu yadda yake jami'an da ke aiki a sashin bincike na marabar Ikotun yayin da aka kawo masa karar misalin karfe 7:00 na daren 15 ga watan May, 2022.
A cewarsa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Yayin da naje asibitin da aka garzaya da marigayin, na gan shi a gadon tura mara lafiya da sharbeben yanka a kirjinsa, yana kwance ba rai. Haka zalika, ya ga wanda ke kare kansa wanda shima ya samu kananan raunuka, yana zaune a gaban asibitin da wuka a hannayensa.
"Ya ce yana so ya kara dabawa wasu mutanen makamin, amma tawagar da ni muka amsa wukar cikin dabara daga garesa gami da kaishi ofishinmu.
“Akwai mutane da dama a wurin, wadanda yawancinsu yaran Hausawa ne a gaban asibitin, inda na tambayi ba'asi suka shaidamin yadda aka kama wanda ake karar yayin da yayi yunkurin tserewa.
"Na kai wanda ake karar wani asibiti kusa da ofishinmu don kula da raunukan da ya samu. Mun dauki jawabinsa yayin da muka dauki jawabin 'dan uwan marigayin.”
Ya cigaba da cewa:
"Bincike ya bayyana yadda marigayin, yayin da wasu daga cikin 'yan hayan da wanda ake karar suke da matsala kan kudin NEPA inda wanda ake zargin ya ki biyan N1,000.
"Wanda ake zargin cikin fushi ya shiga gida ya fito da wukar yanke-yanke ya dabawa marigayin a kirjinsa, bayan sabanin.”
- A cewarsa.
Yayin da tawagar bincike tayi nazari game da lamarin, Mr Wale Ademoyejo, shaidar ya ce ya dauki tsawon shekaru 20 yana aikin 'yan sanda, kuma ya rubuta jawabin ga wanda ke kare kansa saboda baya cikin natsuwa.
"Wanda ke korafin ya ce, yayin da wanda ake karar ya dauki wuka, duk 'yan hayan suka fita daga dakin amma marigayin ya matsa kusa da shi.
"Mai karar, yayin rubuta jawabinsa, ya ce wanda ake karar ya dabawa marigayin makami a harabar gidan amma yayin da mu ka je gidan, babu daya daga cikin 'yan hayan da ya shirya rubuta jawabi, hakan yasa bamu kama kowa ba.
Tsohon Saurayi Ma Shekaru 97 da Bai Taba Aure ba Yayi Caraf ya Aure Budurwa Mai Shekaru 30 a Kayataccen Biki
"Na kira mai daukar hoto don ya dauki marigayin a asibitinsu, sai dai ba zan iya cewa wannan kisan kai bane saboda wanda ake kara ya tabbatar da shi ne ya dabawa marigayin makami.”
- A cewar shaida.
Asali: Legit.ng