Tashin Hankali Yayin da Jami’an Hukumar DSS Uka Mamaye Ofishin Gwamnan CBN

Tashin Hankali Yayin da Jami’an Hukumar DSS Uka Mamaye Ofishin Gwamnan CBN

  • Hukumar tsaro ta farin kaya ta yi mamaya a ofishin gwamnan babban bankin CBN bisa wasu laifuka
  • A baya an bayyana yadda hukumar ke farautar gwamnan bisa zargin ya dauki nauyin ayyukan ta'addanci a kasar nan
  • Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana ko sun yi nasarar kame gwamnan ba, kasancewar a baya kotu ta hana su kama shi

FCT, Abuja - Jami'an hukumar tsaro na farin kaya (SSS) a ranar Litinin da yamma sun dura hedkwatar babban bankin Najeriya (CBN), inda suka mamaye ofishin gwamna babban banki, Godwin Emefiele.

Jaridar leadership ta ruwaito cewa, akwai wata dambarwa tsakanin hukumar ta SSS da gwamnan CBN Emefiele, inda hukumar ke zarginsa da daukar nauyin ta'addanci.

Idan baku manta ba, hukumar a baya ta bukaci umarnin kotu don kwamushe gwamnan, lamarin da bai samu ba, kasancewar an hana SSS kamawa, gayyata ko tsare gwamnan.

Kara karanta wannan

Albishir ga 'yan Najeriya: Karon farko a wata 11, hauhawar farashin kayayyaki ya yi kasa

DSS ta mamaye ofishin gwamnan CBN
Tashin Hankali Yayin da Jami’an Hukumar DSS Uka Mamaye Ofishin Gwamnan CBN | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

An ce Emefiele ya kasance a kasar waje na tsawon lokaci a hutunsa na karshen shekara da zai kare a ranar 17 ga watan Janairun 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya zuwa yanzu dai kakakin hukumar ta SSS Peter Afunanya bai yi karin haske game da wannan mamayar ba.

A mamayar da jami'an suka yi yau, Daily Post ta ce an gansu da yawa a motoci sama da 20 a hedkwatar babban bankin da ke birnin tarayya Abuja.

Kotu Ta Hana Hukumar DSS Da EFCC Kama Emefiele Gwamnan CBN

A tun farko, wata kotu a Najeriya ta hana hukumar tsaron ta DSS da kuma EFCC kame gwamnan na CBN.

Alkali M.A. Hassan, mai shari'a a babban kotun da ke zama a Abuja ne ya hana hukumomin biyu kama gwamnan.

Hukumomin suna zargin gwamnan da aikata badakala da kuma daukar nauyin ta'addanci, lamarin da ya dauki hankalin 'yan Najeriya da dama.

Kara karanta wannan

Saura Kwana 40 Zabe, Manyan Yan Takara Atiku da Kwankwaso Sun Yi Babban Rashi a Arewacin Najeriya

Hakazalika, kotun ta hana a gayyaci Emefiele, ko bincikarsa ko ma dai yi masa barazana da ka iya jawo tsaiko gare shi.

Rikicin Emefiele da majalisar kasa

A watan Disamban bara, majalisar kasa ta gayyaci gwamnan domin tattauna wasu batutuwa da suka shafi tattalin arzikin kasa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, majalisar ta so tattaunawa ne da shi kan kayyade adadin kudaden da mutum zai iya cirewa a asusu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.