Yan Bindiga Sun Kai Wa Dan Takarar Majalisar Wakilai Hari, Sun Kashe Yayansa kuma an Jikkata Yan'uwa
- Ana saura yan kwanaki zabe ana cigaba da kai hare-hare kan yan takara musamman a kudancin Najeriya
- Wasu yan bindiga sun dira gidan wani dan takarar majalisa kuma sun hallaka yan uwansa
- Dan takarar ya ce yana zargin gwamnan jihar ta Imo da daukan nauyin wadannnan yan bindiga
Yan bindiga da adadinsu ya kai hamsin sun kai mumunar hari gidan dan takarar kujerar majalisar wakilai kuma Kakakin gamayyar jam'iyyun siyasa, Ikenga Imo Ugochinyere.
Yan bindigan sun dira gidansa dake Akokwa, karamar hukumar Ideoto North ta jihar Imo ranar Asabar, 14 ga Junairu, 2023.
Tuni an bindige babban yayansa, Ikeagwuonu, har lahira kuma wasu yan'uwansa da dama sun jikkata, rahoton Leadership.
Kalli hotunan gidan:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Nnamdi Kanu: Buhari Ba Ya Ganin Kimar Ibo, In Ji Ɗan Takarar Majalisa Na PDP
Dan takarar jam'iyyar PDP na mazabar Ideato a Jihar Imo, Ikenga Ugochinyere, a ranar Juma'a, ya ragargaji Shugaba Muhammadu Buhari, biyo bayan cigaba da tsare shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, duk da kotu ta bada umurnin sakinsa sau uku.
Kotun daukaka kara a Abuja ta bada umurnin sakin Kanu kan zargin ta'addanci da aka shigar a kansa, The Punch ta rahoto.
Babban kotun tarayya, a Umuahia, ita ma ta bada umurnin a saki Kanu, ta umurci gwamnatin tarayya ta mayar da shi Kenya inda aka dako shi ba bisa ka'ida ba.
Babban kotu a Abia ita ma ta yanke hukunci na sakin shugaban na IPOB.
Ugochinyere, wanda shine kakakin 'Coalition of United Political Parties cikin wani sanarwa, ta ce cigaba da tsare Kanu duk da umurnin kotun ya nuna cewa gwamnati ba ta girmama doka.
Ya kara da cewa lamarin hujja ne da ke nuna Shugaba Buhari bai ganin mutane Ibo da kima.
Asali: Legit.ng