Wazirin Bauchi Da Aka Kwancewa Rawani Ya Shigar Karar Gwamnatin Bauchi Kotu

Wazirin Bauchi Da Aka Kwancewa Rawani Ya Shigar Karar Gwamnatin Bauchi Kotu

  • Iyalan Alhaji Muhammadu Bello Kirfi sun shigar da gwamna Bala Abdulkadir Mohammed kotu
  • Gwamnatin jihar Bauchi ta tsige Alhaji Bello Kirfi daga majalisar sarkin Bauchi kuma ta kwance rawaninsa
  • Bello Kirfi ya kasance tsohon dan siyasa wanda ya rike mukamai lokacin Shagari da Obasanjo

Bauchi - Tsohon Minista, Bello Kirfi, ya shigar da karar gwamnatin jihar Bauchi kotu bisa kwance masa rawani a matsayin Wazirin masarautar Bauchi mai dimbin tarihi.

An kwancewa Bello Kirfi rawani ne bisa rashin biyayya da girmama gwamnan jihar, Bala Mohammed Abdulkadir.

Kirfi ya rika kujerar minista karkashin mulkin marigayi tsohon shugaban kasa Shehu Shagari da kuma mulkin Olusegun Obasanjo.

Bello Kirfi
Wazirin Bauchi Da Aka Kwancewa Rawani Ya Shigar Karar Gwamnatin Bauchi Kotu Hoto: UCG
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai magana da yawun Bello Kirfi kuma 'dansa, Yakubu Kirfi, ya bayyana cewa sun shigar da kara domin kwatowa mahaifinsu hakkinsa, rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban APC Na Kasa Ya Fasa Kwai, Ya Ce Zaben Shugaban Kasa Yana da Naƙasu

Yace:

"Lamarin cireshi matsayin Wazirin Bauchi kuma dan majalisar sarki a ranar 3 ga Junairu 2023, aikin gwamnatin jihar ne kuma tayi amfani da masarautar; wannan abu ya tada kura a cikin jihar."
"Mutane daga ciki da wajen jihar sun yi layin zuwa gidan Alhaji Muhammad Bello Kirfi domin jajanta masa da kuma nuna masa goyon baya, kuma mun gode."
"Saboda haka lamarin na gaban kotu yanzu wanda zai yanke hukunci kan abinda gwamnati tayi."

Yakubu ya yi watsi da rahotannin cewa mahaifinsa ya lashi takobin cire gwamnan a zaben 2023 saboda shi ya kawo shi ofis, riwayar RipplesNigeria.

A cewarsa:

"Wannan labarin boge ne, babu gaskiya ciki."
"A matsayinmu na Musulman kwarai, mun aminci mulki na Allah ne kuma shi ke baiwa wanda ya ga dama kuma ya kwace lokacin da yaga dama."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: