N40 Ake Biya: Matashi Ya Bayyana Rasit Din Kudin Makarantarsa na 1994
- Wani mutumi 'dan Najeriya, Sir Jarus, a dandalin Twitter ya dora gami da bayyana irin arhar da kudin makarantar da yayi karatu yayin da yake tasawa
- A wallafarsa, ya bayyana yadda ya biya N40 a JSS 1 a 1994 da kuma N1,090 na komai da ya shafi karatunsa duk da hayar daki a jami'a a 2001
- A cewarsa, jimillar kudin da ya kashe a ilimin Boko daga firamare zuwa jami'a bai kai N200,000 ba
Wani mutumi 'dan Najeriya mai suna Sir Jarus ya bayyana kididdigar kudin da ya kashe na gaba daya rayuwar makarantarsa a matsayinsa na dalibi.
Kamar yadda ya bayyana, ya biya N40 a matsayin kudin makaranta yayin da yake ajin farko a sakandiri (JSS 1) a shekarar 1994.
Bayan ya samu gurbin karatu a Jami'ar Obefemi Awolowo, ya biya kudi N1,090 a shekararsa ta farko a jami'a (100 level) a matsayin kudin da ya kunsa duk wani abu da ya shafi karatu da kuma matsugunni a shekarar 2001.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kara da bayyana yadda ya kashe kimanin N15,000 a shekararsa ta karshe a jami'a. Jarus ya ce gaba daya kudin da ya kashe daga matakin firamare zuwa sakandiri bai kai N200,000.
Kamar yadda ya rubuta:
"Kudin makarantar zango na daya a shekarata ta farko a sakandiri N40 (Naira arba'in) a 1994. Na biya N1,090 (Dubu daya da naira cassa'in) a matsayin kudin makaranta da matsugunni a shekarar 2001.
"Na biya 15,000 ko kusan haka a shekarata ta karshe. Gaba daya jimillar kudin da na kashe a ilimin Boko na daga matakin firamare zuwa kammala jami'an bai kai N200,000."
Martanin 'yan soshiyal mediya
@sharperleinado ya ce:
"Najeriya tayi kokari kuma tana cigaba da kokarin da da yawa daga cikinmu. Dukkanmu mun amfana ta wani wurin ko wani gurin."
@VOluwayemi yayi tsokaci:
"Nayi imani duk da irin arhar da kayi karatu hakan ba yana nufin iyayenka sun biya kudin makarantarka cikin sauki ba a lokacin ku a makaranta. Gaba daya karatun da nayi a Ìfe bai kai N50,000 ba nima.
"Ilimi kyauta ne a makarantar gwamnati, a firamare na da sakandiri."
@KalimatSuleiman ya kara da cewa:
"Yanzu suna son kwace wannan damar daga daliban Najeriya tare da 'janyo tsadar ilimi' - kamar bashi ga dalibai bayan kara kudin makaranta yadda da yawa ba za a iya biya ba gami da datse tallafin a ilimin makarantar gaba da sakandiri."
@yemileel ya ce:
"Gaskiya tayi matukar arha yallabai."
@segun_are ya ce:
"Ilimi ba zamba bane. Ka narka kasa da N200,000 amma kana girbar daruruwan bandira."
Rasit ya nuna Dantata yana cikin 'yan Najeriya na farko da suka fara zuba kudi a banki
A wani labari na daban, wani tsohon rasit da ya bayyana a Twitter ya nuna yadda Alhaji Alhassan Dantata ya zama cikin 'yan Najeriya na farko da suka fara zuba kudadensu a banki.
A wancan lokacin, bankin Turawa ne aka bude wanda yanzu shi ake kira da First Bank.
Asali: Legit.ng