An Kulla Yarjejeniyar Babu Kula Saurayi Tsakanin Wani Uba da Karamar Diyarsa, Bidiyon Ya Yadu

An Kulla Yarjejeniyar Babu Kula Saurayi Tsakanin Wani Uba da Karamar Diyarsa, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani uba ya kulla yarjejeniya da karamar diyarsa wanda zai hana ta soyayya da namiji har sai ta kai shekaru 20 da doriya
  • Wani mai amfani da Facebook Emmanuel Stephen ya wallafa bidiyon uba da diyar tasa suna shiga yarjejeniyar
  • Yayin da hakan ya burge wasu iyaye maza, wasu sun sanar da uban cewa akwai hanyoyi da dama kewaye da haka

Yayin da ake samun shakuwa mai karfi tsakanin iyaye maza da ‘ya’yansu mata, tunanin yadda rayuwarta za ta kasance ta bangaren soyayya baya taba barin zuciyar mutum har sai ya faru.

Wani uba ya samawa kansa mafita ya hanyar kulla yarjejeniyar babu kula saurayi.

Uba da 'ya
An Kulla Yarjejeniyar Babu Kula Saurayi Tsakanin Wani Uba da Karamar Diyarsa, Bidiyon Ya Yadu Hoto: Emmanuel Stephen
Asali: Facebook

Babu abun da ya fi mallakar da ni’ima a duniyar nan. Sai dai kuma su kan zo da tarin nauyi da gajiyarwa lamarin da kan jefa iyaye cikin damuwa muddin rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Sabon Salo: Wata Amarya Ta Yi Amfani da Maza 5 a Matsayin Kawayenta Ranar Biki, Bidiyon Ya Ja Hankali

Wani mai amfani da Facebook Emmanuel Stephen ya wallafa wani bidiyo na wani uba da ke kulla yarjejeniya da karamar diyarsa cewa ya haramta mata soyayya har sai nan da 2041.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da kallon kyakkyawar yarinyar, za ka fahimci cewa zuwa lokacin Za ta kai irin shekaru 20 da ‘doriya, shekarun fara soyayya.

Masu amfani da soshiyal midiya sun fahimtar da uban cewa ta yiwu an yi wasa da hankalinsa ne

Yayin da bidiyon ya burge wasu iyaye maza tare da wayar masu da kai, wasu sun sanar da mutumin cewa ba lallai wannan ya yi tasiri ba.

Idan ka mallaki diya wacce ta girma ko matashiya, toh za Ka san cewa wannan bidiyon ba komai bane. An ji kunya, koda dai tunanin na da dadi.

Jama’a sun yi martani

Mzwandile Simondwana ya ce:

Kara karanta wannan

Ya Yi Sa’a: Matashiyar Baturiya Ta Kai Saurayinta Dan Najeriya Gida Don Iyaye Su Gani, Ta Rangada Masa Girki

“Ina ji a jikina cewa za a karya wannan yarjejeniyar.”

Ezeh Michael ya ce:

“Idan za a kulla yarjejeniya, dole a samu wakilai daga bangarori biyu tare da fahimtar juna amma a nan ina iya ganin cewa uban da mai daukar kamara sun yaudari wannan kyakkyawar Muna neman ayi mata adalci ya zama dole a sake bitar abun.”

Funmi Layo ta ce:

“Da ta dauki hayar tawagar lauyoyi don su taimaka. Da alama bata ga komai ba ta wannan gilashin rage hasken rana.”

Sladjana Prica ta ce:

“Hahah hadadden uba...bari mu sa ran cewa ya kula da tsoffin yan matansa cikin mutuntawa saboda abun da kayi za a maka..”

Freddy Scar Moncar ta ce:

“Tana kallon yarjejeniyar da kyau. Tana tunani ta yi kuskure.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng