Mutumin Da Ya Auri Mata 8 Da Yara Fiye Da 50 Zai Ginawa ‘Ya’yansa Makaranta Su Kadai
- Kedel ya kasance magidanci mai tarin iyali inda yake da matan aure takwas da yara fiye da 50
- Magidancin wanda ka iya kara aure a gaba yana shirin gina makaranta wanda yaransa kawai ne za su dunga halarta
- A tsarin aurensa, karamar matarsa ce ke da alhakin nema masa amarya ta gaba da zai yi
Wani magidanci mai suna Kadel wanda ya auri mata takwas kuma yake da yara fiye da 50 yana shirin ginawa yaransa makaranta wanda su kadai za su dunga zuwa.
Za a gina makarantar ne a kusa da gidansa. Afrimax English wacce ta rahoto labarin mutumin ta bayyana cewa dalilinsa na yin haka ya kasance saboda akwai tazara sosai tsakanin gidansa da makarantar yaransa.
Kadel ya kuma bayyana tsadar kai yaransa makaranta a matsayin wani dalili da yasa yake son gina masu makaranta.
Sabon Salo: Wata Amarya Ta Yi Amfani da Maza 5 a Matsayin Kawayenta Ranar Biki, Bidiyon Ya Ja Hankali
Shi ne zai dunga biyan malaman albashi. Mutumin na zaune lafiya da matansa kuma bai rufe kofar kara aure ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar Afrimax, hakkin matarsa ta karshe ne nema masa amarya ta gaba da zai yi. Kafar labaran ta bayyana cewa matan basa kishi da junansu kuma suna kula da yaransu daidai.
Jama’a sun yi martani
Naphatie ta ce:
“Me yasa matan suka yi kamar zautattu kuma basa farin ciki amma shi yana cikin farin ciki da annashuwa.”
Wendy Mckay ta ce:
“Talauci zai sa mata yin komai, da yana da arziki me zai sa yaransa sanya yagaggun kaya.”
Litchie Litch ta ce:
“Ina mai ba da hakuri kan halin da magabata na suka shiga amma na gode Allah ba a haife ni ba a inda irin haka ke faruwa."
ChristChrysalislnMahanaim ya ce:
"Ina fatan zai kara wasu gonaki don iyalinsa su wadata.."
A wani labarin, wani magidanci da ke da yara 102 da jikoki 568 a kasar Uganda ya yanke shawarar daina haihuwa.
Musa Hasahya mai shekaru 67 a duniya da matan aure 12 ya bukaci matan nasa da su fara amfani da magungunan hana daukar ciki don su samu su dunga cin abinci.
Mutumin wanda manomi ne ya ce suna matukar wahala shi da iyalinsa wajen samun na sakawa a bakin salati.
Asali: Legit.ng