Kai Tsaye: Yadda Yakin Neman Zaben APC a Jihar Adamawa Ke Gudana

Kai Tsaye: Yadda Yakin Neman Zaben APC a Jihar Adamawa Ke Gudana

Jirgin yakin neman kujerar shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 na jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress APC ya garzaya Adamawan Lamido, Arewa maso gabashinNajeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari, dan takarar shugaban kasan APC, Asiwaju Bola Tinubu; abokin tafiyarsa, Kashim Shettima; Shugaban uwar jam'iyyar, Adamu Aliyu da sauran jiga-jigai sun dira Yola.

Sauran sun hada da gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; Gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru; Bashir Ahmed, dss.

Buhari ya daga hannun Tinubu da Binani

Shugaba Muhammadu Buhari ya daga hannun Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da yar takarar gwamnan jihar Adamawa, Aishatu Dahiru Binani.

Buhari ya bayyana cewa ba zai yi wata doguwar jawabi mai tsawo ba.

Yace:

"Ina so na muku bayani. Na kawo muku wanda jam'iyyarmu ta yadda da shi ya zama shugaban kasa, shine Ahmed Bola TInubu. Ku zabeshi zai yi mana aiki a nan kasar yadda ya kamata. Zai rike amana."
"Mutanen Adamawa ku zabi Binani tayi muku gwamna. Adamawa zakuyi abinda ba'a taba yi ba. Ba'a taba zaben mace ta zama shugaba, zaku zabeta. Mu APC muna goyon bayanta kuma Inshaa'aLlahu zata ci nasara, Nagode kwarai da gaske."
Dan Allah Don Annabi ku fiddamu kunya ku zabesu

Adamawa Sai Binani, Jawabin Tinubu a wajen kamfen Adamawa

Dan takara kujerar shugaban kasa, Ahmed Bola Tinubu, a jawabinsa na yakin neman zabe a Yola ya ce dole ne a dama da mata a mulkinsa kuma yana tare da yar takarar gwamnan jihar, Aisha Binani dari bisa dari.

Tinubu ya ce idan al'ummar Adamawa na son farin ciki, cigaba, ayyuka, jin dadi, to su zabi Aisha Binani.

Tinubu ya caccaki jam'iyyar PDP, ya ce sunansa jam'iyyar cigabar talauci watau Poverty Develoment Party.

Ya yi kira ga yan Najeriya kada su kuskura su zabi PDP. Ya yi alkawari ga yan Najeriya cewa idan aka aka zabesu zasu yi mulki na kwarai.

Kalli cikakken bidiyon a nan, rahoton TVC:

Amaechi ya halarci taron jihar Adamawa

A karon farko tun da aka fara kamfen yakin neman shugaban kasa na APC, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya halarci na jihar Adamawa.

An kwana biyu ana rade-radin cewa Amaechi ya yi hannun riga da kamfen tun bayan shan kashi a zaben fidda gwani a 2022.

Shugaba Buhari ya dira jihar Adamawa

Kamar yadda yayi alkawari, shugaba Muhammadu Buhari tare da tawagarsa sun dira jihar Adamawa domin yakin neman zaben shugaban kasan APC.

Online view pixel