Bayan Tsare Dokpesi a Filin Jirgin Sama na Amurka, An Sako shi

Bayan Tsare Dokpesi a Filin Jirgin Sama na Amurka, An Sako shi

  • Jami'an hukumar kula da shige da fice na kasar Amurka, sun saki Raymnd Dokpesi, mataimakin darakta janar na tawagar kamfen din Atiku Abubakar
  • An rahoto cewa, jami'an sun hanzarta kiran Dokpesi daga saukarsa a Amurka tare da rike shi na tsawon sa'o'i a ranar Lahadi
  • Jigon jam'iyyar PDP din ya dira kasar ne bayan gwamnatin Birtaniya ta kira Atiku kan wasu lamurra da suka shafi zaben watan gobe

Hukumar gidan talabijin din AIT tace shugaban kamfanin sadarwa na Daar, Raymond Dokpesi, an sako shi daga hannun hukuma bayana tsare sa da aka yi a filin jirgin sama na Heathrow da ke Landan.

Raymond Dokpesi
Bayan Tsare Dokpesi a Filin Jirgin Sama na Amurka, An Sako shi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, jami'an hukumar kula da shige da fice sun dakatar da Dokpesi a yayin da yake hanyarsa ta zuwa Frankfurt a jirgin kamfanin Lufthansa da ya isa Ingila.

Kara karanta wannan

Munanan Bayanai Sun Bullo a kan Dalilin Cafke Mutumin Atiku da Aka Yi a Kasar Ingila

"Dokpesi ya sauka ta Frankfurt daga Abuja a jirgin saman kamfanin Lufthansa kuma an kira shi daga jirgin kafin sauran fasinjojin su sauka."

- Hukumar gidan talabijin din ta sanar a ranar Litinin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"An dakatar da Dokpesi na tsawon sa'o'i a filin jirgin saman kafin a saka wa fasfotinsa hatimi kuma jami'an hukumar kula da shige da ficen suka ba shi damar shiga kasar."

Jaridar TheCable ta rahoto cewa, takardar ta kara da cewa, jigon jam'iyyar PDP din ya kama hanyar Landan ne bayan gayyatar Atiku Abubakar da gwamnatin Birtaniya tayi kan wasu lamurran da suka shafi zaben da za a yi a watan gobe a Najeriya.

Dokpesi shi ne mataimakin darakta janar na tsarika da fasaha na tawagar kamfen din shugaban kasa na PDP.

'Yan sandan Landan sun magantu

Kara karanta wannan

Da Dumi-duminsa: Hoton Atiku Cikin Murmushi Ya Bayyana Yayin da Ake Rade-radin Bai Da Lafiya

TheCable ta tuntubi Metropolitan Police Service a Landan kan faruwar lamarin amma sun ce ba za su iya bada wannan bayanin ga jama'a ba.

Morgan, wata jami'ar hudla da jama'a da tayi magana da TheCable, tace ya zama dole kada ta fitar da rahoton wannan kamen inda ta kara da cewa ba za ta iya bayar da tabbacin halin da ake ciki ba ko ma an yi kamen.

A bangarensa, Debo Ologunagba, kakakin babbar jam'iyyar adawa ta PDP ya sanar da TheCable cewa ba shi da tabbacin wannan kamen.

An kama Sanata Ekweremadu da matarsa a Landan

A wani labari na daban, 'yan sandan Landan sun yi ram da Sanata Eke Ekweremadu a Landan tare da matarsa kan zargin yunkurin cire sassan jikin wani don ceto lafiyar diyarsu mai fama da ciwon koda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng