Baturiya Ta Kai Saurayinta Dan Najeriya Gida, Ta Gabatar Da Shi Ga Danginta, Ta Rangada Mai Girki a Bidiyo
- Wata Baturiya ta garzaya soshiyal midiya don nunawa mutane yadda ta gabawar iyayenta saurayinta dan Najeriya a lokacin Kirsimeti
- Kyakkyawar yarinyar ta tabbatar da ganin cewa saurayin ya sake a gidansu yayin da ya hadu da yan uwanta
- Mutane da dama da suka yi martani sun bayyana cewa matashin ya yi dace yayin da wasu suka bukaci ta kula da shi
Wata matashiyar Baturiya ta wallafa bidiyon da ke nuna lokacin da ya kai saurayinta dan Najeriya ya hadu da danginta a lokacin Kirsimeti.
Matar ta bayyana cewa koda dai ta san cewa matashin ya yi nesa da gida, tana son yin duk wani abu da sai sa shi jin kamar a gida yake.
Budurwa ta kula da saurayinta
A wani bidiyo da ya tara dubban martani, budurwar ta nunawa duniya saurayinta. Bayan ta gabatarwa iyalin da abinci a kan tabur, sai duk suka zauna suka yi raha.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yayin da gaba daya iyalin ke tattaunawa da matashin, sai suka kunna wakar Burna Boy suna sauraro a TV.
Kalli bidiyon a kasa:
A daidai lokacin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya samu martani fiye da 500 da ‘likes’ fiye da 19,000.
Jama’a sun yi martani
Kai ya ce:
“Sanin kaina zan kare da tambayar a ina lewandiski yake da zama.”
DanieanKemet ya ce:
“Dan uwa na da jarumta.”
osmondamu ya ce:
“Irin wannan yarinyar namiji yake bukata. Dan uwa ya yi sa’a.
Alexei Aleksandra ta ce:
“Ina fatan kin ji dadin bikin Kirsimeti da yan uwanki.”
Nathan Onyeka ta ce:
“An gode da kika tayamu kula da shi...Naija ta duniya.”
Big Bear ya ce:
“Dan Allah ki kula da yarona.”
Uba ya goya diyarsa a bayan wani butun-butumi
A wani labari na daban, jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan sun yi karo da bidiyon wata karamar yarinya da aka barwa mahaifinta ya yi renonta bayan mahaifiyarta ta fita unguwa.
Yarinyar dai ta sako mahaifin nata a gaba da fitina inda ya dauke ta ya goyawa wata butun-mutumi yayin da shi kuma ya koma yana rarrashinta da fatan tsira daga hannun mahaifiyarta idan ta kama shi a kan haka.
Asali: Legit.ng