Yan Sanda Sun Dakile Yunkurin Sace Kakakin Majalisar Dokokin Filato

Yan Sanda Sun Dakile Yunkurin Sace Kakakin Majalisar Dokokin Filato

  • Dakarun yan sanda sun dakile shirin wasu 'yan bindiga na yin awon gaba da kakakin majalisar dokokin jihar Filato
  • A wata sanarwa, hukumar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce maharan sun yi kokarin shiga gidan kakakin
  • Kwamishina ya bayyana jin daɗinsa kana ya gode wa al'umma bisa taimakon da suke baiwa jami'ai

Plateau - Jami'an hukumar yan sandan jihar Filato sun yi nasarar dakile yunkurin wasu da ake zaton masu garkuwa ne na awon gaba da shugaban majalisar dokokin jihar, Yakubu Sanda.

Vanguard ta rahoto cewa maharan dauke da makamai sun biyo sawun kakakin Majalisar da misalin karfe 11:30 na dare a wata motar Honda CR-V har zuwa gidansa da ke Low-Cost, Jos.

Yan sanda a Filato.
Yan Bindiga Sun Dakile Yunkurin Sace Kakakin Majalisar Dokokin Filato Hoto: vanguard
Asali: UGC

Sai dai yunkurin maharan dake cikin Motar na kutsa kai cikin gidan da sace shugaban bai kai ga nasara ba saboda jajircewar yan sanda masu gadi da kawo ɗaukin DPO na Caji Ofis din Rantya a kan lokaci.

Kara karanta wannan

An Tsaurara Tsaro A Yola Babban Birnin Jihar Adamawa Gabanin Zuwan Shugaba Buhari Yakin Neman Zabe

Bayanai sun nuna cewa shugaban caji Ofis din, SP Ayuba Iliya, da dakarunsa sun yi hanzarin zuwa suka hada karfi da 'yan sanda masu gadin gidan har suka yi nasarar dakile shirin miyagun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake tabbatar da lamarin a wata sanarwa, mai magana da yawun hukumar yan sandan Filato, DSP Alfred Alabo, yace:

"Dabarun da kwamishinan yan sanda ya bullo da su sun fara haifar da ɗa mai ido a yan kwanakin nan. A lokacin nan sun taimaka wajen dakile yunkurin garkuwa da kakakin majalisa, Hon. Yakubu Sanda."
"A ranar 6 ga watan Janairu, bayan shugaban ya isa gidansa na Jos, wasu 'yan bindiga uku a ciki motar CR-V Jeep suka biyo sawunsa da nufin shiga gidan su yi gaba da shi."
"Amma burinsu bai cika ba bayan yan sanda masu gadi sun ankara da kuma kawo daukin gaggawa daga Caji Ofis din Rantya, inda DPO da tawagarsa suka hada karfi suka dakile maharan."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Je Har Gida, Sun Harbe Shugaban Jam'iyya Har Lahira

Wane mataki aka dauka bayan lamarin?

Alabo ya kara da cewa tuni rundunar yan sanda ta bazama ta ko ina domin zakulo wadanda suka kulla harin da kamo su, kamar yadda Channels ta ruwaito.

Kwamishinan yan sanda ya jinjina wa daukacin al'umma bisa nuna damuwa da abubuwan dake faruwa da taimaka wa jami'an tsaro da sahihan bayanai.

A wani labarin kuma Miyagun 'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban YPP Na Gunduma a Jihar Imo

Wasu tsagerun Yan bindiga sun harbe shugaban jam'iyyar YPP na wata gunduma a jihar Imo har rai ya yi halinsa.

Ganau ya ce maharan sun zo a motoci biyu kuma ana zargin yan banga ne domin sun tafi da gawarsa zuwa FMC, sun ce dan bindiga ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262