An Samu Hatsaniya A Masallacin Marigayyi Dr Ahmed BUK A Yayin Sallar Juma'a
- Shararren malamin da yai suna kuma yake da cibiyar koyar da hadisan Manzon Allah Salllahu Alaihi Wassalam a jihar Kano
- Cibiyar ta Darul-Hadith ba iya masallaci bane harda makarantar Islamiya da Boko da kuma dakin karatu
- Tun bayan rasuwa abubuwa suka taya a makaranta sabida samun sabani a tsakanin mabiyansa da almajiransa kan wanda zai jagoranci cibiyar
Kano - An samu hautsini a cibiyar ilimi ta Darul Hadith (Wadda take kunshe da masallaci, makaranta da dakin karatu) ta shararren malamin addinin Musuluncin marigayyi Sheik Ahmed Bamba
Rikicin ya fara ne tun lokacin da Allah yayi shararren malamin addinin musuluncin rasuwa kuma hakan yasa ba'a samu wanda zai maye gurbinsa sabida sabani da ake samu a tsakanin mabiyansa ko almajiransa.
Al'amarin da ya faru yau ya faru ne yayin da na'ibin limimanin ke kkokarin hawa munbarin hudubar sallah Juma'a aka samu wasu suka fizgoshi daga kan mumbarin da kuma yunkurin hanashi jan sallah.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Lamarin yayi kauri inda sai da jami'an tsaron yan sanda suka ka kai dauki wajen wajen sasanta al'amarin sannan kuma suka rufe masallacin.
Mallam dai ya rasu ne a shekarar data gabata 2022, bayan fama da gajeruwar jinya a asibitin kwararru na mallam Aminu Kano dake Kwaryar birnin Kano.
Allah ya karbi ran Shararren malamin Addinin nan Wato Dr Ahmed BUK
Shararren malamin addinin musulunci nan da yakre rayuwarsa wajen karantar da al'umma hadisan Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wassalam ya kwanta dama.
Malamin ya rasu ne a farkon watan shekarar data gabata a ranar Juma'a wato bakwai ga watan Janairun shekarar 2022
Malamin ya rasu rasu yana da shekara 82 a duniya, kuma yana da 'ya 'ya da mata da dama wanda adadinsu ya kai kusan 36
Dr Ahmed BUK ko kuma Dr Ahmed Bamba ko qala haddasana shine sunan da yai kaura suna dashi.
Asalin Dr
Dr Ahmed BUK dan asalin kasar Ghana wanda yayi kuriciya acan ya samu damar zuwa jami'ar musulunci ta Madina Inda yai karatu kan Hadisan Manzon Allah Sallalahu alaihi Wassalam a digiri na farko dana biyu dana uku
Ya dawo Kano inda ya fara koyarwa a jami'ar BUK, daga nan ne kuma ya ajiye aiki tare da bude cibiyarsa mai suna Darul Hadith Salafiyya dake Tudun yola.
Asali: Legit.ng