Rigimar Limanci Ta Kawo Tsaiko a Sallar Jumu'a a Masallacin Marigayi Sheikh Ahmad BUK

Rigimar Limanci Ta Kawo Tsaiko a Sallar Jumu'a a Masallacin Marigayi Sheikh Ahmad BUK

  • Rikici kan shugabanci a Masallacin Darul Hadith da ke Tudun Yola a Kano ya kawo cikas yayin Sallar Jumu'a ranar 6 ga watan Janairu
  • Sahihan bayanan da muka samu sun nuna cewa bayan matsalar da aka samu, jami'an yan sanda sun ba da tsaro har aka gama Sallah
  • Kakakin yan sanda, Abdullahi Kiyawa, yace tuni aka gayyaci bangarorin biyu domin lalubo bakin zaren

Kano - Rigima kan shugabanci a Masallacin Darul Hadith na marigayi Sheikh Dakta Ahmad Ibrahim BUK dake Tudun Yola a Kano, ta kawo tsaiko yayin gudanar da Sallar Jumu'a ranar 6 ga watan Janairu, 2023.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa rigimar ta ɓarke ne lokacin da wasu daga cikin manyan Masallacin suka hana sabon Limami wucewa, yayin da zai shiga ya hau Mimbari don jagorantar Sallar Jumu'a.

Kara karanta wannan

2023: Ali Nuhu, Zango da Manyan Taurarin Kannywood na Goyon Bayan Tinubu

Masallacin Darul Hadith.
Rigimar Limanci Ta Kawo Tsaiko a Sallar Jumu'a a Masallacin Marigayi Sheikh Ahmad BUK Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wasu bayanai da ake yaɗa wa sun nuna cewa fusatattun mutanen sun hana Limamin hawa Mimbari ya yi huduba, lamarin da ya kawo tsaiko yayin Sallar mai dumbin falala.

Limamin, wanda aka tsara zai jagoranci Sallar a jiya, ya kama hanyar shiga wajen da aka ware wa Liman a Masallacin, ba zato mutanen suka tare shi, an ce har rigarsa suka rike.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakamakon wannan takaddama da aka samu, nan take jami'an tsaro suka shiga tsakani, suka kewaye Masallacin don tabbatar da doka da oda, hakan ya sa wasu Masallatan suka kama gabansu.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, yace ba tare da bata lokaci dakarun 'yan sanda suka kai ɗauki bayan samun kishin-kishin din abinda ke faruwa.

Kara karanta wannan

An Kama Amina Guguwa Yar Shekara 50 Kan Kashe Kishiyarta Yayin Dambe A Bauchi

"Nan take Kwamishinan yan sanda ya umarci a tura karin jami'ai Masallacin domin tabbatar da bin doka da oda."
"Jami'an sun dawo da komai kan hanya kuma an gudanar da Sallah ba tare da wata matsala ba. A halin yanzun hukumar 'yan sanda ta gayyace bangarorin biyu domin gano bakin zaren."

- Abdullahi Kiyawa.

Tuni dai mazauna yankin Amguwar Tudun Yola suka ci gaba da harkokin gabansu bayan abinda ya faru a Masallacin.

Dalibai mata a BUK sun sake shiga tasku

A wani labarin kuma Barayi Sun Shiga Dakin Kwannan Dalibai Mata A Jami'ar Bayero Da Ke Kano

Jami'ar dai ta dawo daga hutun kirsimeti da sabuwar shekara a farkon satin nan da muke ciki wanda hakan yasa akwai karancin dalibai a dukunan kwanan.

An ce barayin sun shiga Hostel din Nana Hall, suka yi barna mai tarin yawa da ta hada da sace wayoyi da wasu kayan amfanin dalibai.

Kara karanta wannan

Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Sheka ‘Dan Bindiga, Sun Kama Yaran Turji, Kachalla da Tukur

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: