An Kashe Sufeto ’Yan Sanda Da ’Yan Bindiga a Yayin Wani Artabu Da ’Yan Ta’adda a Nasarawa

An Kashe Sufeto ’Yan Sanda Da ’Yan Bindiga a Yayin Wani Artabu Da ’Yan Ta’adda a Nasarawa

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta yi rashin babban jami’i yayin musaya da wasu tsagerun ‘yan bindiga
  • An hallaka wasu ‘yan bindiga biyu yayin wannan musaya da ta dauki dan lokaci ana yi a hanyar Akwanga zuwa Jos
  • An nemi mazauna da su zauna lafiya, su kuma kai rahoton duk wani motsi na ‘yan bindiga da suka gani a yanki

Akwanga, jihar Nasarawa - Wani Sufeton ‘yan sandan, Yusuf Jafaru ya rasa a yayin artabu da tsakanin ‘yan sanda da ‘yan bindiga a kusa da titin Akwanga-Jos a jihar Nasarawa.

Wakilin Punch ya tattaro cewa, lamarin da ya yi sanadiyyar dan sandan da wasu ‘yan bindiga biyu ya faru ne a daren ranar Laraba a garin Nunku da ke karamar hukumar Akwanga a jihar.

An ruwaito cewa, ‘yan bindiga da suka zo da yawansu, sun bude wuta kan wasu jami’an ‘yan sanda biyar da ke aikin sinitiri a yankin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Mazauna sun rikice, an sace musu mai gidan saukar baki

Dan sanda da 'yan bindiga 2 sun mutu a Nasarawa
An Kashe Sufeto ’Yan Sanda Da ’Yan Bindiga a Yayin Wani Artabu Da ’Yan Ta’adda a Nasarawa | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

An ajiye gawar jami’in da ya rasu a bakin aiki a babba asibitin Akwanga yayin da aka jefe gawarwakin ‘yan bindigan kuma a ofishin ‘yan sanda a garin na Akwanga.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar wannan lamarin a yau Juma’a 6 ga watan Janairu a birnin Lafia ta bakin kakakin rundunar, Ramhan Nansel.

A cewarsa:

“Abin da ya faru a Akwanga ya faru ne a ranar 4 ga watan Janairu, 2023 da misalin karfe 9 na dare, tsageru sun farmaki jami’anmu da aka tura kan titin Akwanga-Jos daidai farin Nunku.”

Hukumar ta yi kira ga mazauna yankunan da su ci gaba da bin doka da oda kuma su ci gaba da yin kasuwancinsu na halal.

Hakazalika, ta bukaci mazauna da su zuba ido kan jama’a, kana su maida hankali don gano masu dauke da raunukan harbin bindiga, kana su kai rahoto ga ‘yan sanda.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: ‘Yan Ta’adda Sun Kai Hari kan Matafiya, Sun Harbi Kwararren ‘Dan Jarida

Direba ya buge dan sanda ya gudu a Legas

A wani labarin kuma, wani mai mota ya lallaba, ya banke dan sanda ya fece da gudu a wani yankin jihar Legas.

Wannan lamari ya tada hargitsi, an cunkoso da yawa a inda hadarin ya faru, za a dauki mataki.

Rundunar ‘yan sanda ta yi Allah wadai da wannan lamari, ta bayyana bukatar daukar mataki cikin gaggawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.