An Samu Gawar Wasu Magidanta A Jihar Kano Bayan Amfani da Gawayi Dan Jin Dumi

An Samu Gawar Wasu Magidanta A Jihar Kano Bayan Amfani da Gawayi Dan Jin Dumi

  • Sakamakon yadda aka shigo hunturu sosai, mutane na amfani da hanyoyi masu yawa domin dumama jikinsu ko ninda suke zaune
  • Hukumomin kashe gobara sun sha bada shawara samar da wadatacciyar zagayawar isak a indan za'a dumama din ko kuma inda aka sa wutar
  • Gobara da tashe-tashen wuta dai sun fi kamari a lokacin hunturu sabida yadda isaka take kadawa

Kano - Rundunar yan sandan jihar kano sun tabattar da samu gawar wasu magidanta a karamar hukumar Dawakin Tofa ta jihar kano.

Mai magana da yawun hukumar yan sandan DSP Abdullahi Harune ya tabbatar da faruwar hakan ta bakin wakilin The Cable, a wata sanar wa da yayi jiya laraba yace cewa an kawo rahotan batan wasu magidanta tun 2 ga watan Janarun wannan shekarar,

Gawayi
An Samu Gawar Wasu Magidanta A Jihar Kano Bayan Amfani da Gawayi Dan Jin Dumi Hoto: The Cable
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Dan Siyasa Da Wasu Mutane Uku a Wata Jahar Kudu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce bincike ya nuna magidantan sun rasu ne sakamakon sarkewar numfashi wanda ta sanadiyar gawayin da suka kunna ne a dakinsu dan jin dumi.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Abdullahi na cewa

"Mun samu rahoto a ranar 3 ga watan Janarun wannan shekarar wajen karfe 9:00, daga wani kauye mai suna Kwa a karamar hukumar Dawakin Tofa, cewa ba'a ga wasu magidanta ba ko kuma basu fito daga gidansu ba tun ran 2 ga watan Janairu, kamar yadda wasu suka ce sun rabu da su a ranar 2 ga watan da misalin karfe 11 na dare

Su Waye magidantan da suka rasa ransu?

Magidanta mata da miji da ake ce sunansu Sulaiman Idris da Maimuna Halliru kamar yadda jaridar The Cable ta rawaito

Kakakin yan sandan kano ya ce:

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Hayaki Ya Turnuke Wasu Ma’aurata Har Lahira a Kano

"Lokacin da kakar idris tai kokarin bude kofar dakin da suke, sai ta lura cewa magidanta suna kwance a kan gado basa motsi kuma ga alamar wani kauri na fitowa daga dakin da suke."
"Da jin wannan batu kwamishinan yan sandan jihar kano Mamman Dauda ya umarci shashin bincike na musamman wanda CSP Ahmed Hamza baturen yan sandan karamar hukumar ya jagoranta dan gano musabbabin abinda yai sanadiyar rasa ransu
"An dauke gawar magidantan tare da garzayawa da su asibitin kwararru na Murtala, inda kuma anan ne bincike ya tabbatar da cewa sun mutu

Sun mutu ne sakamakon hayakin da suka shaka wanda yake a gurbace, kuma hayakin ya fito ne daga jikin gawayin da suka kunna domin jin dumi a dakinsu, kamar yadda binciken likitoci ya nuna inji Kiyawa

Daqga karshe Kiyawa yana mai bawa magidanta shawara kan su san yadda zasu yi amfani da abubuwan jin dumi a dakinsu da kuma kula da yadda za'a sasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida