‘Yan Ta’adda Sun Farmaki Matafiya a Kogi, Sun Harbi ‘Dan Jarida

‘Yan Ta’adda Sun Farmaki Matafiya a Kogi, Sun Harbi ‘Dan Jarida

  • Wasu miyagun ‘yan ta’adda sun kai wa motocin matafiya mugun farmaki kan babban titin Lokoja zuwa Obajana da ke jihar Kogi
  • Rahoto ya bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun harbi wani ‘dan jarida na musamman na Daily Trust kuma an garzaya dashi asibiti
  • Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, William Aya yace zasu tura jami’ai yankin don babbar hanya ce kuma basu riga sun san abinda ke faruwa ba

Kogi - Kwararren ‘dan jarida mai aiki da Daily Trust, Idowu Isamotu, an harbe shi kan babban titin Lokoja zuwa Obajana dake jihar Kogi, jaridar Punch ta rahoto.

Harbin miyagu
‘Yan Ta’adda Sun Farmaki Matafiya a Kogi, Sun Harbi ‘Dan Jarida. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Jaridar Punch ta rahoto yadda farmakin da ‘yan bindiga suka kai musu wurin karfe 5 na yammacin Laraba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

An karya lagon tsageru: An yi bata kashi da 'yan bindiga, an hallaka tsageru 4 nan take

A sakon da Punch ta samu, an kwatanta miyagun da ‘yan ta’adda.

Yace:

“Yanzun nan ‘yan ta’adda suka harbe ni kan babban titin Lokoja zuwa Obajana. Allah kadai ya kare mu.
“Ina motar kai na. Mu hudu ne manyan maza da kananan yara biyu a motar.”

An kai su asibiti a yayin da ake rubuta wannan rahoton.

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, William Aya, yace zai sanar da ‘yan sandan dake kusa a kan babbar hanyar Lokoja zuwa Obajana.

Aya yace:

“Zan kira dukkan ‘yan sandan dake kan babban titin. Babbar hanyar Lokoja zuwa Obajana doguwa ce, don haka sai na tuntubi DPO duk dake yankin kafin in bada rahoton halin da ake ciki.”

Karin bayani na nan tafe…

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng