Kotu ta Aike Wa da Ƙani Gidan Yari Kan Janye Hankalin Matar Aure a Kano

Kotu ta Aike Wa da Ƙani Gidan Yari Kan Janye Hankalin Matar Aure a Kano

  • Wata kotun shari'a ta Kano a ranar Laraba, tayi umarni da sakaya wa da 'kani gami da wata Hassana Surajo a gidan yari bisa zarginsu da yin sharholiya da matar aure
  • Ana tuhumar wadanda ake zargin da jerin laifuka uku na janye hankali, hure kunne da kuma sharholiya da matar aure
  • An gano yadda daya daga cikin ukun, Saifullahi ke hira ta WhatsApp gami da kai wa matar auren, Fatima Alhassan ziyara da sunan shi 'dan uwanta ne bayan sun taba soyyaya a baya

Kano - Wata kotun shari'a dake Kano a ranar Laraba tayi umarni da sakaya wa da 'kani, Saifullahi Hamisu da Mujahid Hamisu tare da wata Hassana Surajo a gidan kaso bisa zarginsu da jan hankalin wata matar aure.

Kurkuku
Kotu ta Aike Wa da Ƙani Gidan Yari Kan Janye Hankalin Matar Aure a Kano. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa, wadanda ake karar, suna zaune ne a Bachirawa Kwatas Kano, kuma ana tuhumarsu da jerin laifuka uku na janye hankali, hure kunne da kuma sharholiya da wata matar aure.

Kara karanta wannan

Dirama, Wani Dan Kasuwa Ya Hargitse a Kotun Musulunci Kaduna, Yace Yana Kaunar Matarsa

Mai gurfanarwa, Aliyu Abideen ya bayyanawa kotu yadda wani Ahmad daga Fagge Kwatas na Kano ya kaiwa korafin ga SCID Bompai Kano a ranar 22 ga watan Disamba, 2022.

Abideen ya kara da labarta yadda a wannan ranar da misalin karfe 4:00 na yamma wadanda ake zargin ba tare da izini ba ya auka gidan wanda ke karar a Dorayi Kwatas, Kano.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Wadanda ake zargin sun fake da zama 'yan uwan matar mai karar (Fatima Alhassan).
"Sakamakon haka, wanda ke karar ya gano yadda mutum na farko cikin ukun da yake kara Saifullahi yana soyayya da matarsa kuma suna hira a kafar Whatsapp.
"Bayan shi Saifullahi tsohon saurayin matar wanda ke karar ne."

Saifullahi ya musanta laifin da ake tuhumarsa yayin da na biyu da na ukun da ake kara suka amsa laifukansu.

A cewar alkali mai shari'a, laifin yaci karo da dokar shari'a ta jihar Kano.

Kara karanta wannan

2023: Gaskiya Ta Fito, Gwamnan APC Ya Magantu Kan Rahoton Yana Yi Wa PDP Aiki

Sannan kotu tayi umarni da sakaya wadanda ake karar a gidan yari, gami da daga sauraron karar zuwa 17 ga watan Fabrairu, don cigaba da sauraro.

Kotu ta yankewa 'dan Hisbah hukuncin kisa

A wani labari na daban, wata babbar kotu dake zama a jihar Kano, ta yankewa wani tsohon jami'in hisbah hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan an kama shi da laifin kashe bazawararsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng